in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin na fatan matasa za su kara yin himma da kwazo
2019-04-30 20:01:42 cri


Ran 4 ga watan Mayu, rana ce ta matasan kasar Sin. A gabanin wannan rana, wato yau Talata a nan Beijing, an shirya wani gagarumin taron cika shekaru 100 da matasa suka yi zanga-zangar neman dimokuradiyya da ilmin kimiyya.

A jawabinsa yayin bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga matasa da su kaunaci kasarsu da kuma tausayawa bil Adama baki daya. Ya kuma bukaci matasa da su nuna biyayya ga al'adun Sinawa na daukar daukacin bil Adam tamkar iyali guda, da kuma mayar da hankulansu kan harkokin al'umma domin kara hammatuwa wajen farfado da al'ummar Sinawa baki daya, sannan su yi kara kokari wajen kara bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kafa kyakkyawa makoma ga bil Adama gaba daya.

A ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919 ne, wasu malamai da dalibai matasa na kasar Sin suka kaddamar da wata babbar zanga-zanga, da ta karade wurare daban daban na kasar, don neman kubutar da al'ummar Sin daga mawuyacin halin da take fuskantar a lokacin, inda 'yan kasar da yawa suka amsa kiran da aka yi musu na gudanar da zanga-zanga da yajin aiki, da ba da taimako ga ayyukan kishin kasa. Ta wannan babbar zanga-zanga ce aka fara yada ra'ayin Markisanci a kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping na ganin cewa, zanga-zangar da aka yi a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919, ba ma kawai ta taimaka wajen kaddamar da juyin-juya hali a fannin al'umma, da aikin wayar da kan jama'a, da na daidaita al'adu a kasar Sin ba, har ma ta sa Sinawa fara kama hanyar neman farfado da al'ummarsu. A cewar shugaba Xi, tarihi ya sheda mana cewa, matasan kasar Sin suna da babban buri, da matukar kishin kasa, da kwarewa a fannin kirkiro sabbin fasahohi. Saboda haka, a ko da yaushe su ne ke taka muhimmiyar rawa a kokarin farfado da al'ummar kasar Sin.

Kawo yanzu, shekaru 100 da suka wuce, an shiga wani sabon zamanin farfadowar al'ummar kasar Sin, a don haka an bukaci matasan kasar da su sauke sabon nauyin dake bisa wuyansu, ciki har da ci gaba da nuna hali nagari na "zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayu", wanda ke mayar da hankali kan kishin kasa, ana iya cewa, duk wani Basine a nan kasar Sin yana kishin kasarsa, musamman ma matasan kasar dake rayuwa a sabon zamanin da ake ciki, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu babbar ma'anar kishin kasa ita ce kishin kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma salon tsarin gurguzun mai sigar kasar Sin baki daya.

Yau kasar Sin tana murnar cika shekaru 100 da gudanar da aikin kishin kasa na ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919, ko "May Fourth Movement" a Turance, kana za ta yi murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin. Sakamakon yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje cikin shekaru 40 da suka wuce, ya sa kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Ta fita daga matakin koma-baya da wulakanci da ta fuskanta yau shekaru 100 da suka wuce. Duk da haka yayin da muke kokarin farfado da al'ummar Sinawa a halin yanzu, akwai bukatar matasan kasar su yi gwagwarmaya da sauke nauyin da aka dora musu. Salibi da haka ne Shugaba Xi Jinping ya bukaci matasa da kada su daina gwagwarmayar da suke yi.

A hakika, ko da yaushe Sinawa matasa na mai da hankali kan daukaka gwagwarmaya. Yanzu suna kirkiro sabbin abubuwan al'ajabi da duk duniya ke mamaki saboda matukar kokari da kuma basirarsu. A shekaru uku da suka kwashe suna aiki a kasar Serbia, manajoji Sinawa 9 na kamfanin samar da karafa na Hebei na kasar Sin, wadanda matsakaicin shekarunsu ya kai 39 da haihuwa, sun sa masana'antar kera karafa ta Smederevo ta samu riba a maimakon faduwa sakamakon yadda suka hada kai tare da ma'aikata 500 na masana'antar, har ma masana'antar ta zama mafi girma wajen daukar ma'aikata da yawan kayayyakin da ta fitar zuwa ketare. Sun kuma bayyana cewa, za su yi kokarin bunkasa masana'antar da ta zama mafi karfi a fannin takarar samar da karafa a Turai.

Bayan kowane shekaru dari, duk lokacin da kasar Sin ke bikin tunawa da zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayu, a kan saka wasu sabbin abubuwa a ciki sakamakon canjin zamanin da aka samu. A shekaru ukun da suka wuce, jaridar New Times ta wallafa wani sharhi mai taken The World's Big Problem: Young People, wato matsala mafi tsanani a duniya ita ce Matasa, a wani mataki na fadakar da shugabannin kasashen duniya cewa, muddin aka daidaita batutuwan da suka shafi matasa, za'a samar da kyakkyawar makoma.

A hakika, shugaban kolin kasar Sin wato Xi Jinping ya mai da hankali sosai kan ayyukan na matasa, tare kuma da sada zumunta da matasa na bangarori daban daban, wadanda suka hada da matasa na Sin da na kasashen ketare, kullum yana ambaton cewa, "kasa tana da karfi idan matasa suka ci gaba". Kwanan baya, ya rubuta wasika ga daliban wata makarantar sakandare ta kasar Amurk dake koyon Sinanci, don ba su amsa, inda ya kara musu gwarin gwiwa wajen koyon Sinanci. Ya ce, idan har suka koyi Sinanci za su fahimci kasar Sin da kuma sada zumunci tare da wadanda ke iya Sinanci na kasashe daban daban. A cikin nasarorin da aka cimma a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu da aka kammala ba da dadewa ba, yawan ayyukan hadin kai da gwamnatin kasar Sin ta shugabanta sun kai guda 26, guda biyar daga ciki na da nasaba da matasa.

Raya matasan Sin masu kyakkyawan halaye a dukkan fannoni da kokarin raya tsarin gurguzu na Sin, muhimmin aiki ne dake shafar makomar kasar Sin. Game da wannan batu, shugaba Xi Jinping ya bukaci kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatoci da bangarori daban daban na kasar su saurari ra'ayoyin matasa da nuna musu goyon baya da kuma nuna musu hanyar samun ci gaba da ta dace. Ya jaddada cewa, an raya kasar Sin mai tsarin gurgurzu na zamani don cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin, kamar wasan gudu mika sanda. Ya kuma yi imani cewa, wasan gudu yana da kyau, kana yana fatan matasa za su ci gaba da yin wasan gudu, har su samu wani kyakkyawan sakamako a nan gaba. (Sanusi, Bello, Jamila, Tasallah, Kande, Murtala, Bilkisu, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China