in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Lee Group na kasar Sin na kokarin bunkasa sana'o'i a Najeriya
2019-04-30 15:27:33 cri


A halin yanzu tarayyar Najeriya da kasar Sin na gudanar da hadin-gwiwa sosai a fannoni daban-daban, kuma wasu kamfanonin Sin masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sana'o'in kasar, ciki har da kamfanin Lee Group mai hedkwata a yankin Hong Kong. Kawo yanzu, kamfanin Lee Group ya riga ya bude masana'antu da dama a Najeriya, tare kuma da samar da guraban ayyukan yi masu tarin yawa ga jama'ar kasar.

A jihar Jigawa dake kusa da birnin Kano, akwai wata sabuwar masana'antar samar da takalma da kamfanin Lee Group ya kafa a watan Fabrairun bana, mai suna kamfanin Vinylon Footware Industry Limited, inda ma'aikatan wurin ke nuna himma da kwazo wajen gudanar da ayyukan samar da takalma. A ko wace rana, masana'antar na iya samar da ire-iren takalma da yawansu ya kai dubu dari.

Zhou Mingfu shi ne shugaban masana'antar samar da takalma ta Vinylon Footware Industry Limited. Zhou, mutumin birnin Shanghai na kasar Sin ne, wanda ya yi shekaru 23 yana aiki a Najeriya. Yayin da ya tabo magana kan hadin-gwiwar Sin da Najeriya, Zhou Mingfu ya bayyana cewa:

"A ganina bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya', ana kara samun mutanen kasar Sin wadanda suke zuwa Najeriya, kuma yanayin tsaro na dada inganta a Najeriya. Gwamnatin tarayya gami da jama'ar kasar suna maraba da zuwanmu mutanen Sin. Wannan abu na da muhimmanci, saboda yayin da muke rayawa, gami da zuba jari a cikin sana'o'in wurin, za mu samar da guraban ayyukan yi da yawa. Bayan da aka bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya', kamfaninmu ya samu habaka, har mun taimaka musu wajen warware matsalolinsu na rashin ayyukan yi da kayayyaki, don haka yana da muhimmancin gaske. Za mu kuma godewa goyon-bayan da jam'iyyar kwaminis gami da gwamnatin kasar Sin take ba mu."

Hussein Garba, ma'aikaci ne mai shekaru 22 a masana'antar Vinylon Footware Industry Limited dake Kano ya bayyana cewa:

"Yayin da muke gamuwa da kalubale, kwararrun kasar Sin su kan taimaka mana wajen daidaita su. Takalman da muke samarwa a nan, ana sayar da su a sassa daban-daban na Najeriya, kuma kamfaninmu ya dauki 'yan kasa da dama don su yi aiki a nan."

Kamfanin Lee Group ya fara zuba jari da kafa masana'anta a Najeriya a shekara ta 1962. Kawo yanzu, baya ga manyan masana'antun samar da takalma, kamfanin ya kuma kafa masana'antun samar da roba, da fata, da mulmula karafa, da samar da siminti, da burodi da sauransu a sassan arewaci gami da kudancin tarayyar Najeriya, kuma yanzu sun fara zuba jari don kafa lambun noman rake, da masana'antar sarrafa sukari. Babban manaja mai kula da masana'antun arewacin Najeriya na kamfanin Lee Group Li Guowei ya bayyana cewa:

"Lambun noman rake da masana'anar sarrafa sukari da muke kafawa yanzu a jihar Jigawa, za su iya samar da guraban ayyukan yi dubu biyar, kuma wannan masana'antar samar da takalma ta yiwa jama'ar kasar sama da 1200 hanyar samun aikin yi. Ina dalilin da ya sa gwamnatin wurin ta yi maraba da kamfaninmu a fannin zuba jari? Ko a bangaren kere-kere, ko a bangaren noma, duk suna maraba da zuwanmu, saboda muna iya taimaka musu wajen bunkasa tattalin arziki, gami da kyautata zaman rayuwar al'umma."

Daya daga cikin manyan jami'an kamfanin Lee Group masu kula da bangaren noma dake Najeriya Bawa Abubakar, ya taba karatu a kasar Sin na tsawon shekaru bakwai, wanda hakan ya sa ya ji yaren Sin. Ya bayyana cewa:

"A halin yanzu hadin-gwiwar Sin da Najeriya na gudana yadda ya kamata. Yanzu muna shirye-shiryen kafa wata masana'antar samar da sukari, gami da bunkasa ayyukan noman shinkafa, a gani na wannan zai taimaka ga bunkasa kasarmu Najeriya. Mutanen Sin gami da kamfanonin kasar, sun bada babbar gudummawa ga ci gaban Najeriya, al'amarin da zai taimaka ga ci gaban ayyukanmu, wato ke nan hadin-gwiwarmu da kasar Sin na da makoma mai haske."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China