in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaya za mu yi don raya zaman rayuwa maras gurbata muhalli?
2019-04-29 14:38:34 cri
A kwanakin baya, akwai labarai biyu da suka jawo hankalin kasa da kasa sosai. Na farko shi ne yadda kasar Philippines ta nuna fushi ga shara da dama da suka zo daga kasar Canada, ta ce ya kamata Canada ta dawo da sharar, idan ba haka ba, za a yi yaki da kasar. Labari na biyu shi ne, kasar Malaysia ta ki karbar sharar da suka zo daga kasar Amurka, ta ce bai kamata kasashe masu ci gaba su maida kasar Malaysia a matsayin wurin zubar da shara ba.

Batun kawar da shara ba batu ne mai girma ba, amma idan ba a daidaita shi yadda ya kamata ba, hakan na iya kawo matsaloli da dama, har ma za a kai ga rikice-rikice ko yake-yake a tsakanin kasa da kasa. Wannan ya shaida cewa, bai kamata a zubar da shara ga sauran kasashe don cimma burin raya zaman rayuwa maras gurbata muhalli ba. Ya kamata a bi tunanin samun ci gaba, tare da kiyaye muhalli don samar da kyakkyawan yanayin zamantakewar al'umma mai kiyaye muhalli.

A jiya Lahadi, an kaddamar da bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na shekarar 2019 mai taken "Zaman rayuwa maras gurbata muhalli, domin kafa kyakkyawan muhalli" a nan birnin Beijing, inda kasashe da kungiyoyin duniya 110 suka gabatar da sabbin tsire-tsire fiye da 1200 a gun bikin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani game da tarihin raya aikin kiyaye muhalli na Sin, don yin kira ga kasa da kasa da su raya zaman rayuwa maras gurbata muhalli, da kuma raya kyakkyawar al'umma ta dan Adam.

Raya zamantakewar al'umma tare da kiyaye muhalli yana daya daga cikin bukatun da Sinawa ke neman cimmawa tun daga lokacin da. A tarihin kasar Sin, an taba hana yanke itace a lokacin bazara, ko hana kamun kifi a lokacin zafi da sauransu.

Koda yake bunkasuwar masana'antu ta kawo wadata ga dan Adam, amma an fuskanci matsalar gurbata muhalli. Babu shakka wasu kasashe da dama sun gamu da irin wannan matsala a cikin shekaru da suka gabata, ciki har da kasar Sin.

Tuni Sin ta fara tunawa da tsarin raya tattalin arziki, da fara raya aikin kiyaye muhalli. A shekarar 2012, an shigar da aikin kiyaye muhalli a cikin tsarin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasar Sin karo na farko, a gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18. Jama'ar kasar Sin sun nuna goyon baya ga tunanin shugaba Xi Jinping na "Kyakkyawan muhalli ya kawo arziki" a shekarun baya baya nan. A shekarar 2018, an rubuta aikin kiyaye muhalli a cikin gyararren kudin tsarin mulkin kasar Sin.

Mutane da dama suna ganin cewa, ana bukatar gurtaba muhalli yayin da ake yin kokarin raya tattalin arziki. Amma Sinawa da dama sun yi tsammani cewa, ya kamata a nemi wani tsarin daidaito tsakanin samun ci gaba da kiyaye muhalli. Game da wannan batu, Sin ta samu moriya daga gare shi, kana ta yi kokarin aiwatar da shi. Yawan jarin da Sin ta zuba a fannin makamashi masu tsabta ya kai matsayin farko a duniya a shekaru da dama a jere, kana Sin ta fi yin amfani da makamashi masu tsabta da makamashin da ake sake yin amfani da shi. Wannan ya sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin Sin daga tushe. Hakan ya shaida cewa, kyakkyawan muhalli na iya kawo bunkasuwa da wadata.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, dan Adam na tinkarar kalubalen kiyaye muhalli tare, babu wata kasa da za ta iya daidaita shi da kanta ba. Matsala mafi jawo hankalin kasa da kasa ita ce sauyin yanayin iska. Wasu tsibirai suna fuskantar barazanar karuwar leburin teku, kana yanayi maras kyau na kawo illa ga wasu kasashe. Babu shakka, ya dace kasa da kasa su dauki alhakinsu na tinkarar sauyin yanayi tare.

An bude bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na shekarar 2019 na Beijing, bayan da aka gama dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu, inda shugabanni masu halartar taron suka cimma daidaito kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hanyar bude kofa da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hada kasa da kasa, kana ta hada jama'arsu gaba daya, domin samun ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba, wanda ke shafar moriyar jama'a a halin yanzu, har ma da kyakkyawar makomar dan Adam. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China