in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya bayyana sakamakon da aka samu a yayin taron koli na biyu na BRF
2019-04-29 14:18:04 cri
Daga ranar 25 zuwa ranar 27 ga wata, an yi nasarar kiran taron koli karo na biyu na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" wato BRF a birnin Beijing. Mamban majalisar gudanwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya bayyanawa manema labarai sakamakon da aka samu a yayin taron, a jiya Lahadi.

Wang Yi ya ce, idan aka duba jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, da hadaddiyar sanarwar da taron kolin ya bayar, da ma jerin sakamakon da aka samu a yayin taron, za a iya gano manyan sakamako shida da aka samu.

Na farko shi ne an tabbatar da burin kyautata ayyukan raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da ma hanyar hadin kai. Na biyu, za a raya dangantakar abota tsakanin kasa da kasa ta cudanyar juna domin samun ci gaba tare. Na uku shi ne, a samu dimbin sakamako na a zo a gani domin moriyar juna. Na hudu, a samar da dandali ga sassan kasuwanci domin habaka damar hadin gwiwa. Na biyar, a kyautata tsarin hadin kai kan shawarar domin kara samar da goyon baya. Na shida kuma na karshe shi ne a yada alfanun dake tattare da mu'amala tsakanin shugabanin domin zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa.

Ban da wannan kuma Wang Yi ya ce, taron kolin na da babbar ma'ana, wato ya jaddada aniyar raya tattalin arzikin duniya bisa ra'ayin bude kofa, kuma ya bude wani sabon shafi ga aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", baya ga hada gwiwa tsakanin Sin da waje domin sa kaimi ga manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida da Sin ke aiwatarwa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China