in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya ta kago sabon tarihin tattalin arzikin duniya mai bude kofa
2019-04-27 21:58:21 cri

Yau Asabar a nan birnin Beijing aka rufe taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2, bayan da aka zartas da hadadden rahoton taron kolin na shugabannin kasashe daban daban. Mahalartan taron sun bayyana cewa, za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa tushen shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za su gina al'umma mai kyakkyawar makoma tare kuma da samun wadata, kana suna sa ran cewa, za su sake shirya irin wannan taro nan gaba domin cimma burin nan.

Idan aka kwatanta wannan taron kolin da na karo na farko da aka kira shekaru biyu da suka gabata, za a lura cewa, sakamakon da aka samu yayin taron na wannan karon sun fi yawa, misali adadin hakikanin sakamakon da aka cimma ya kai 283, ban da haka darajar ayyukan hadin gwiwar da za a gudanar bisa yarjejeniyoyin da aka daddale kan shawarar ziri daya da hanya daya ta kai dalar Amurka sama da biliyan 64. Ko shakka babu, sakamakon da aka samu yayin da ake kokarin raya shawarar sun burge al'ummomin kasashen duniya matuka, duk wadannan sun bayyana cewa, kasashe da al'ummomin duniya wadanda suka amince da shawarar suna kara karuwa cikin sauri, har sun riga sun shiga wanan babban aikin.

Hakika shawarar ziri daya da hanya daya ta dace da bukatun ci gaban tattalin arzikin duniya, yanzu haka ana aiwatar da shawarar lami lafiya ta hanyar yin kirkire-kirkire, lamarin da ya sake shaida cewa, muddin dai aka raya tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, to za a cimma burin samar da wadata ga al'ummomin kasashen duniya baki daya.

A cikin shekaru shida da suka gabata, a karkashin kokarin da bangarori daban daban suke yi, an riga an tsara wani cikakken tsarin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ciki har da yankunan hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa guda shida dake nahiyoyin Asiya da Tuwai, da hadin gwiwa a bangarorin zirga-zirgar layin dogo da hanyar mota da jirgin ruwa da jirgin sama, da sadarwa, da sauransu. kawo yanzu gaba daya adadin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasar Sin kan shawarar ziri daya da hanya daya ya kai sama da 150.

Kyautata ayyukan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ya zama ra'ayin bai daya da bangarori daban daban suka cimma, lamarin da zai taimaka wa aikin raya shawarar bisa neman samun kyautatuwa yayin ya ke ci gaba. A yayin taron koli na wannan karon ma, mahalartar taron sun bayar da Shawarar Beijing ta yaki da cin hanci da rashawa, lamarin da ya shaida kudurin kasar Sin na inganta hadin kai da kasashe daban daban a fannin yakar cin hanci, bisa aniyar tafiyar da harkokin da ya shafi shawarar "ziri daya da hanya daya" bisa doka. Ban da wannan kuma an kafa kawancen kasa da kasa na neman samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, har ma hukumomin kudi na Sin da Birtaniya da Faransa da Singapore sun daddale yarjejeniyar zuba jari kan sana'o'i marasa gurbata muhalli, wadanda suka aza harsashi ga raya ayyuka bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" ba tare da gurbata muhalli ba. Bugu da kari kuma, bangarori daban daban sun amince da shigar da ajandar MDD ta neman samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 cikin shirin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da hada ka'idojin da za su samu karbuwa a duk duniya cikin shawarar, da ma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma da kiyaye muhallin halittu tare, domin kasa da kasa su samu alfanu daga shawarar. Haka zalika, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayar da tsarin kiyasin bashi don neman samun ci gaba mai dorewa, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin za ta yi kokari tare da kasashen da shawarar ta shafa wajen kyautata aikin kula da basusuka domin gudanar da aikin hada-hadar kudi cikin dogon lokaci, ta yadda za a samu dauwamammen ci gaba.

Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta sa kaimi ga kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa domin ta biya bukatun jama'a. Tsohon firaministan kasar Thailand Surakiart Sathirathai ya yabawa shawarar "ziri daya da hanya daya", yana mai cewa, kamar ruwa dake taimakawa kowa da kowa. Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi, ya zuwa karshen shekarar 2018, Sin ta biya kudin haraji dala biliyan 2 da miliyan 400 ga yankunan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya", kana ta samar da ayyukan yi dubu 270. An gudanar da taron 'yan kasuwa masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na farko a wurin taron kolin dandalin tattaunawar. 'Yan kasuwar dake halartar taron sun cimma ayyukan hadin gwiwa da yawansu ya kai dala fiye da biliyan 64. Wannan ya shaida cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta dace da bukatun jama'a na neman rayuwa mai kyau, kuma bai kamata a hana raya ta ba.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya fada cewa, aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ya dace da yanayin tsarin raya tattalin arzikin duniya na bai daya, da biyan bukatun yin kwaskwarima kan tsarin sarrafa harkokin duniya, da kuma biyan bukatun jama'ar kasa da kasa na neman kyakkyawar rayuwa. Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi wanda shi ma ya halarci taron ya yi nuni da cewa, tsarin zartar da ra'ayi na kashin kai zai kara kawo talauci, amma shawarar "ziri daya da hanya daya" ta dace da bukatun jama'ar kasa da kasa. Yayin da ake kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, jama'ar kasa da kasa suna neman kyakkyawar rayuwa ta hanyar raya shawarar "ziri daya da hanya daya".(Jamila Kande Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China