in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakai biyar za su taimaka kan bude kofa a kasar Sin
2019-04-26 21:58:27 cri

Yau Jumma'a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi a yayin taron kolin hadin gwiwa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara himmantu kan aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kana ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kara daukar sabbin matakai guda biyar domin kara bude kofa ga kasashen ketare.

Wannan sabon mataki ne da shugaban kolin kasar Sin ya sanar, tun bayan taron shekara shekara na dandalin Asiya da aka gudana a garin Bo'ao na lardin Hainan dake kudancin kasar, da kuma bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar daga ketare karo na farko, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin na kara bude kofa za ta ingiza ci gaba mai inganci bisa shawarar ziri daya da hanya daya, ita ma za ta samar da sabbin damammaki ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Abu mafi muhimmanci yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya shi ne, hade sassan ci gaba masu tarin yawa, bisa matsayinta na mai gabatar da shawarar, har kullum kasar Sin tana kokarin habaka bude kofa ga ketare, yanzu haka shugaba Xi ya gabatar da matakan kara bude kofa guda biyar ne bisa bukatun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka game da kara bude kofa ga kasashen ketare.

Misali mataki na farko, game da kara habaka kasuwa ga 'yan kasuwa baki, a shekarar bara, kasar Sin ta rage bangarorin da aka hana yin amfani da jarin waje daga 63 zuwa 48, kana ta dauki matakai guda 22 domin kara bude kofa a bangarorin hada-hadar kudi da samar da mota, da jirgin ruwa, da gina layin dogo da aikin gona, da tace sinadarin ma'adinai, da samar da wutar lantarki da sauransu. Yau ma Xi ya sanar da cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara rage bangarorin da aka hana yin amfani da jarin waje, domin ingiza aikin bude kofa a bangarorin aikin samar da hidimar zamani da aikin kere-kere da aikin gona, duk wadannan za su taimaka kan aikin aiwatar da dokar zuba jari ta baki, ta yadda za a samar da muhalli mai inganci ga 'yan kasuwa baki domin su yi takara bisa adalci a nan kasar Sin.

Mataki na biyu shi ne kara hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a fannin tabbatar da ikon mallakar ilmi. Ana yin kokarin tabbatar da ikon mallakar ilmi. A cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta samu nasarori a fannin tabbatar da ikon mallakar ilmi. Xi Jinping ya bayyana a wannan karo cewa, Sin za ta kyautata tsarin dokoki kan tabbatar da ikon mallakar ilmi a dukkan fannoni, da kara tabbatar da moriyar masu mallakar ikon mallakar ilmi na kasashen waje, da yaki da tilastawa sayar da fasahohi, da yaki da laifuffukan kawo illa ga ikon mallakar ilmi da sauransu, wadannan matakai za su biya bukatun kasar Sin na sa kaimi ga raya kasa a fannin kirkire-kirkire, kana za su taimakawa kasa da kasa wajen samun ci gaban kirkire-kirkire tare.

Mataki na uku shi ne kara shigar da kayayyaki da hidima daga kasashen waje. Bikin baje koli na kayayyakin da ake shigowa da su a kasar Sin karo na farko a watan Nuwanba na shekarar bara, ya shaida wa duniya kyakkyawar makomar kasuwar kasar Sin. A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi alkawari cewa, Sin za ta kara rage harajin kwastam, da kawar da kariyar da aka yi ba ta harajin kwastam ba, da kara shigar da kayayyakin gona da hidima masu inganci daga kasashen waje da sauransu. Babu shakka, hakan zai biya bukatun Sinawa na kashe kudi, da sa kaimi ga Sin da kasashen duniya su samu ci gaba cikin daidaici, da kuma kara bude kasuwannin kasa da kasa a kasar Sin.

Mataki na hudu shi ne kara daukar manufofin tattalin arzikin kasa da kasa bisa manyan tsare-tsare. A yayin da ake kokarin raya tattalin arzikin Sin mai inganci, ba za a yi amfani da tsarin shigar da kayyayaki kawai daga kasashen waje ba, tilas ne a yi musayar kasuwannin cikin gida da waje ta hanyar daidaita ka'idoji da manufofin hadin gwiwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin za ta kara daidaita manufofi tare da manyan kasashen tattalin arzikin duniya, za a kaucewa yin amfani da matakin rage darajar musayar kudi, da nuna goyon baya, da shiga aikin yin kwaskwarima kan tsarin hukumar WTO da sauransu, hakan zai sa kaimi ga kasar Sin wajen kara bude kofa ga kasashen waje.

Mataki na biyar shi ne a kara dora muhimmanci kan yadda za a aiwatar da manufar bude kofa ga waje. Sinawa kan ce, darajar alkawari ta yi daidai da dimbin zinari, shugaba Xi shi ma ya nanata cewa, daukar mataki ya fi fitar da jerin ka'idoji, kana yadda ake aiwatar da shiri ya fi muhimmanci. Tun bayan shekarar da ta wuce, yadda aka aiwatar da matakan kara bude kofar kasar Sin ga ketare da Xi ya sanar a yayin taron shekara shekara na dandalin tattaunawar kasashen Asiya na Bo'ao ya shaida yadda kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi.

A cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron na yau, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin ta dora matukar muhimmanci kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da cinikayya da Sin, da ta daddale tare da kasashe daban daban, da kafa tsarin aiwatar da yarjejeniya, da ma gyara da kyautata dokoki bisa bukatun kara bude kofa ga waje. Lamarin da ya shaida cewa, ba ma kawai kasar Sin tana da aniyar fitar da manufofin kara bude kofarta ba, har ma tana da aniyar daukar matakai na a zo a gani don aiwatar da manufofin.

A matsayinsa na aiki mafi girma a duniya don amfana ga jama'a wanda kasar Sin ta gabatar da shi, aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" na cikin wani muhimmin lokaci na aiwatar da shirye-shiryen da abin ya shafa da aka tsara.

Yadda kasar Sin ta kara bude kofarta ga ketare ya sa kaimi ga kyautatuwar aikin raya shawarar, kana ya samar da sabuwar damar ci gaba ga dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya. Duk wanda ke da burin samun saurin ci gaba, bai kamata ba ya yi watsi da damar shiga motar da kasar Sin take tukawa, wadda take samun bunkasuwa mai inganci yadda ya kamata, da ma kara bude kofarta. (Masu Fassara Jamila, Zainab, Kande, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China