in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya sanar da sabbin matakan kwaskwarima da bude kofa yayin taron kolin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa
2019-04-26 19:28:37 cri

Yau Jumma'a aka kaddamar da taron kolin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 a nan birnin Beijing, shugabannin kasashen waje kusan 40, da wakilan da suka zo daga kasashe sama da 150 ne suka halarci taron, lamarin da ya nuna cewa, shawarar tana kara janyo hankalin kasa da kasa.

shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ma ya halarci bikin, kuma ya gabatar da wani jawabi, inda ya jaddada cewa, shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da sabbin damammakin samun ci gaba ga kasashe daban daban a fadin duniya, ta kuma bude wani sabon shafi ga kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, hakikanan abubuwa sun shaida cewa, aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ya samar da damammakin samun ci gaba ga kasashen duniya daban daban, haka kuma ya bude wani sabon shafi ga kasar Sin, yana mai cewa, "Ana tabbatar da matsayar da aka cimma yayin taron kolin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan sha'awar ziri daya da hanya daya karo na farko lami lafiya, har ma kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 150 suka daddale yarjejeniyar shiga shawarar, abu mai faranta rai shi ne babbar manufar gabatar da shawarar ta yi daidai da babbar manufar tsara muradun raya tattalin arziki, da tsarin hadin gwiwa ta MDD da ASEAN, da AU da EU da EEU, wato kawancen hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Turai da Asiya da sauransu, har ta yi daidai da babbar manufar tsara shirin raya kasashen duniya daban daban. A bayyane take cewa shawarar ta kara habaka ci gaban tattalin arzikin duniya, tare kuma da samar da sabon dandalin cinikayya da zuba jari ga kasa da kasa, wadda kowa da kowa zai ci babbar gajiya daga gare ta."

Shugaba Xi ya sake jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya dace a kara sanya kokari domin cimma burin samun ci gaba mai inganci bisa shawarar ziri daya da hanya daya, yana mai cewa, "Ya kamata mu nace ga ka'idojin tattaunawa tsakanin juna, da gina tare da kuma samun moriyar juna, kana ya dace mu gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban, ban da haka, ya zama wajibi mu ci gaba da nacewa ga manufofin bude kofa ga ketare, da kiyaye muhalli da yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za mu cimma burin samun dauwamammen ci gaba bisa shawarar ziri daya da hanya daya a fadin duniya."

Xi ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake aiwatar da shawarar, shi ne yin cudanya tsakanin kasa da kasa, a don haka kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da sauran kasashe duniya, domin kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu.

A cikin jawabin da ya gabatar a cikin mintoci talatin, shugaban kolin kasar Sin Xi, ya nuna babban sahihanci, har ya gabatar da jerin hakikanan matakai, inda ya sanar da cewa, kasarsa za ta fitar da sabbin matakan yin gyaran fuska da bude kofa ga ketare guda biyar domin kara sabon kuzari cikin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, ya ce, "Mataki na farko shi ne kara bude kasuwa ga 'yan kasuwa baki. Na biyu, kara karfafa aikin kiyaye ikon mallakar fasaha, domin tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, na uku, kara shigo da hajoji da hidima daga ketare, na hudu, kara tabbatar da daidaito kan manufofin tattalin arzikin duniya bisa manyan tsare-tsare, na biyar, kara dora muhimmanci kan manufofin bude kofa ga ketare."

Xi ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara rage bangarorin da aka hana yin amfani da jarin da 'yan kasuwan kasashen waje suka zuba, domin taimaka kan aikin bude kofa a bangarorin samar da hidimar zamani, da aikin kere-kere da kuma aikin gona, kana za a samar da karin damammaki ga 'yan kasuwa baki domin su zuba jari a kasar Sin, tare kuma da tabbatar da aiwatar da dokar zuba jari ta baki, ya ce, "Kasar Sin kamfanin samar da kayayyaki ne na duniya, kuma kasuwar duniya ce, yanzu Sinawan da suka kai matsayin masu samun matsakaicin kudin shiga sun fi yawa a duniya, shi ya sa tana da babban karfi a asirce wajen sayayya. Nan gaba za mu kara rage harajin kwastam domin kara bude kasuwa ga ketare, alal hakika muna maraba ga kayayyaki masu inganci daga kasashen ketare."

Xi ya nuna cewa, kasarsa ta dauki matakan kara bude kofa ga ketare ne bisa bukatun ci gaban kasar, yana sa rai cewa, kasashe daban daban a fadin duniya za su samar da muhallin zuba jari mai inganci ga 'yan kasuwar kasar Sin, haka kuma za su samar da damammaki masu adalci ga kamfanoni, da dalibai, da masana na kasar domin su gudanar da cudanya tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, ko shakka babu kasar Sin tana cike da imani cewa, kasar Sin mai bude kofa za ta kawo wadata ga ita kanta, haka kuma za ta kawo wadata ga daukacin kasashen duniya.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, da sauran shugabannin su ma sun gabatar da jawabai a yayin taron kolin, inda suka jinjinawa sabbin matakan yin gyaran fuska, da bude kofa da Xi ya sanar da su matuka, kana sun nuna fatansu cewa, za su sanya kokari tare, domin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China