Shugaban Kenya: Ana fatan shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta karfafa hadin gwiwar Kenya da Sin ta fannin tattalin arziki da cinikayya
A jiya Alhamis, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da ke halartar taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya a nan birnin Beijing, ya bayyana fatan cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta samar da sabon kuzari ga hadin gwiwar kasarsa da kasar Sin ta fannin tattalin arziki da cinikayya, ta yadda al'ummar kasashen biyu za su kara cin moriya.
Ya kara da cewa, bisa ga shawarar ziri daya da hanya daya, hadin gwiwar kasashen biyu na gudana yadda ya kamata, har an fara cin gajiyar wasu shirye-shiryen da ake aiwatarwa, kuma za a aiwatar da karin wasu shirye-shirye.(Lubabatu)