in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron masu masana'antu karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya"
2019-04-26 11:41:33 cri


A jiya Alhamis, an kaddamar da taron masu masana'antu karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin.

Wannan shi ne irinsa na farko da aka shirya a lokacin taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", masu masana'antu fiye da 850 suka halarci taron, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 80.

Taron ya kunshi matakai guda 4, wato taron dukkan mahalarta taron, da bikin kulla yarjejeniyoyi, da tattaunawa tsakanin wakilan kamfanonin Sin da na kasashen waje, da kuma bikin rufewa. Ko da yake wannan shi ne karo na farko da aka shirya irin wannan taron, amma duk da haka manyan kamfanoni ne suka halarci taron, wadanda suke wakiltar fannoni daban daban.

Mansoor Nadeem Lari, shugaban kamfanin ciniki na SRTIDC na kasar Indiya, ya ce kasar Sin ta samar da wani dandali na musamman ga masu masana'antu na kasashe daban daban, ta yadda za su kulla huldar hadin gwiwa. Hakan, a cewarsa, zai ba su damar tabbatar da wasu takamaiman ayyuka. Mista Lari ya ce,

"Shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' ba ta shafi hadin gwiwar da ake yi tsakanin gwamnatoci kawai ba, har ma ta baiwa kamfanoni damar kulla hulda a tsakaninsu. Ina farin ciki sosai, ganin yadda aka samar wannan dandali ga masu masana'antu. Kuma na yi imani cewa, za a samu takamaiman sakamako musamman ma a bikin kulla yerjejeniyoyi."

A nata bangare, Arancha Gonzalez, darektar zartaswa ta cibiyar ciniki ta kasa da kasa, wadda ita ma ta halarci taron, ra'ayinta ya zo daya da na mista Lari. A ganin jami'ar, kamata ya yi, a sanya karin kananan da matsakaitan kamfanoni su shiga a dama da su karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Ban da haka, ta ce, cibiyar ciniki ta kasa da kasa, a matsayinta na kungiyar da ta sa hannu kan yarjejeniyar "Ziri Daya da Hanya Daya", za ta kara goyon bayan kananan da matsakaitan kamfanoni, gami da taimakawa hada masu jari na kasar Sin da damammakin zuba jari dake kasashen waje. Madam Gonzalez ta kara da cewa,

"A lokacin taron baje kolin kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su wanda ya gudana a karon farko a bara, mun gayyaci kanana da matsakaitan kamfanoni fiye da 100 na kasashe fiye da 20 domin su halarci taron. Wadannan kamfanoni sun riga sun fara ciniki da kasar Sin. Daya daga cikinsu har ma ya fara sayar da amfanin gona a kasuwanni daban daban na kasar Sin. Sa'an nan wasu kamfanonin kasashen Nepal da Myanmar kuma sun fara sayar da albarkatunsu na yawon shakatawa da hidamomi a kasar Sin. Irin wadannan Misalai suna da yawa."

Tun bayan da aka gabatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" a shekarar 2013, shekaru 5 ke nan da suka gabata, an samu dimbin sakamakon karkashin shawarar. A cewar shugaban kamfanin Standard Chartered Group, Jose Vinals, shawarar ta zama ginshiki ga yunkurin dunkulewar duniyarmu waje guda. Ya ce,

"Kasashen da suke hadin kai da mu'amala da juna suna iya hadin gwiwa a matakai daban daban, lamarin da zai taimaka ga karuwar ciniki da ci gaban tattalin arziki. Alal misali, yawan kudin cinikin da aka yi tsakanin kasar Sin da sauran kasashen da suka halarci shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' ya karu da kashi 16.3% a shekarar 2018 bisa makamancin lokacin shekarar 2017, jimillar da ta zarce ta cinikin da kasar Sin take yi da sauran kasashe. Ya kamata mu lura da cewa, tattalin arzikin kasashe masu sukuni na tafiyar hawainiya. Saboda haka, shawarar za ta taimake mu a kokarin raya kasuwannin kasashe masu tasowa, musamman ma na kasashen Asiya da na Afirka."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China