Yawan mutum-mutumin inji da kasar Sin ta kera don amfani da su a ayyukan masana'antu ya zarce dubu 150
A shekarar 2018 da ta wuce, yawan mutum-mutumin inji da kasar Sin ta sayar don yin amfani da su a ayyukan masana'antu ya zarce dubu 150, adadin da ya karu da kaso 14.97% bisa makamancin lokacin shekarar da ta gabata. Hakan na nuna cewa, a shekaru shida a jere kasar Sin ta zama kasuwar sayen mutum-mutumin inji da ake amfani da su a ayyukan masana'antu mafi girma a duniya. A sa'i daya kuma, an samu babban ci gaba a fannin nazarin manyan sassan mutum-mutumin inji.