in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" zai shiga wani lokaci na kyautatuwar ayyukansa
2019-04-25 19:07:48 cri

Yau Alhamis aka bude taron koli na dandalin tattauna hadin kai tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a nan birnin Beijing, taron dai na kwanaki uku, ya samu halartar wakilai kusan 5000 daga kasashe fiye da 150, da ma kungiyoyin duniya fiye da 90. Bayan da aka samu saurin ci gaba bisa shawarar a cikin shekaru biyu da suka gabata, an fara mai da hankali kan ingancin aikin raya shawarar da kasar Sin ta gabatar, a matsayinsa na shirin da ya fi samun karbuwa daga al'umma, kuma wanda ya samar da dandali mafi girma ta fuskar hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa.

Ko shakka babu, dalilin da ya sa aka samu saurin ci gaban hakan shi ne himmatuwa da gwamnatin kasar Sin ke nunawa, da ma sa hannu a cikin aikin da al'ummomi ke yi, baya ga yadda kasashen duniya ke bin ka'idar yin shawarwari tare don ci gaba tare, da ma more sakamako tare, da kuma yadda suke amincewa da aiki mai alfanu, wanda kuma ya kunshi kowa da kowa.

Bisa alkaluman da bankin raya Asiya ya tattara, an ce, idan har a yanzu yankin Asiya yana son samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, a kalla yana bukatar jarin dalar Amurka biliyan dubu 26, wanda za a zuba cikin aikin gina kayayyakin more rayuwa, kana shi ma wani rahoton binciken da asusun IMF ya gabatar kwanakin baya ya nuna cewa, a nahiyoyin Latin Amurka da Afirka da sauransu, inda aka fi himmantu ga aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, gina kayayyakin more rayuwa na matsayin muhimmin dalili wanda ke haifar da cikas ga karuwar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma a yankunan.

Duk wadannan sun bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu wato kusan daukacin kasashen duniya suna fama da matsalar gibin kasafin kudi mai tsanani a bangaren gina kayayyakin more rayuwa. Ko shakka babu kokarin da ake yi wajen aiwarar da shawarar ziri daya da hanya daya, zai taimaka ga kawar da matsalar, tare kuma da sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki a fadin duniya.

Tun bayan da aka gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya kafin shekaru 6 da suka gabata, ana gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin bangarori biyu ko uku, ko tsakanin bangarori da dama lami lafiya, duk da cewa, wasu kasashe masu ci gaba ba su daddale yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ba tukuna, amma hakika sun riga sun shiga ayyukan da ake gudanarwa bisa shawarar, ta hanyoyi daban daban. Misali gabatar da shawarwari masu nasaba, da hidimar doka da harkar kudi, ko shiga aiki kai tsaye. Irin wannan hadin gwiwar da ake gudanarwa ya daga matsayin aikin, haka kuma ya kyautata ma'aunin aikin, har ya kai ga aza harsashi mai inganci ga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya a nan gaba.

A sakamakon raya shawarar "ziri daya da hanya daya", wasu kungiyoyi da hukumomin yankuna, sun fara dora muhimmanci kan hada shirye-shiryensu na samun ci gaba, da raya shawarar "ziri daya da hanya daya", kamar su ajandar shekarar 2063 ta kungiyar AU, da shirin hadin gwiwar dake tsakanin Turai da Asiya na kungiyar EU da sauransu.

Babu shakka, wannan hadin gwiwa zai taimakawa ayyukan raya shawarar da kuma shirye-shiryen samun ci gaba na kasa da kasa da yankuna. Wannan zai kasance muhimmin batu ga raya shawarar "ziri daya da hanyar daya" mai inganci.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana sau da dama cewa, an fito da shawarar "ziri daya da hanya daya" a kasar Sin, wanda zai amfani dukkan duniya gaba daya. Yayin da shugabannin kasashe da hukumomin kasa da kasa 39, da masana da shugabannin bangarori daban daban fiye da dubu daya suke tattaunawa a nan birnin Beijing, ana iya fatan cewa, raya shawarar "ziri daya da hanya daya" mai inganci, zai kara samar da damammakin ci gaba ga kasa da kasa. (Kande Jamila Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China