Bana shekaru shida ke nan da aka gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", bisa wannan tsari ne kamfanonin kasar Sin da dama suka habaka ayyukansu a kasashen ketare, har ma suka kammala wasu manyan ayyuka da dama dake jawo hankulan kasashen duniya. Aikin cibiyar raya kasuwanci (CBD) ta sabon babban birnin kasar Masar da kamfanin gine-gine na CCEC na kasar Sin ya dauki nauyin ginawa, wanda zai kasance wani sabon gini dake zama alamar wuri a nahiyar Afirka. An dama da wasu 'yan kasashen Afirka a wadannan ayyukan da kasar Sin ta dauki nauyin ginawa. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani ne game da wata ma'aikaciya 'yar kasar Masar da ta shafe shekaru 31tana aiki a kamfanin CCEC.