in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara bude kofa a bangaren binciken sararin samaniya
2019-04-24 20:22:03 cri

Yau Talata 24 ga watan Aflilun shekarar 2019, ranar raya aikin binciken sararin samaniya ta hudu ce ta kasar Sin, inda aka gabatar da albishiri da dama, misali kasar Sin ta sanar da sabon ci gaban gina tashar bincikenta a sararin samaniya, kana an bayyana cewa, kawo yanzu gaba daya adadin kumbunan da kasar Sin ta harba zuwa sararin samaniya cikin nasara ya riga ta kai 12, a sa'i daya kuma, ta harba na'urar binciken Tiangong-1, da dakin gwajin dake sararin samaniya wato Tiangong-2. Ban da haka ta kai 'yan sama-jannati guda 14 sararin samaniya a cikin kumbuna 11, ta kuma dawo da su cikin nasara.

Yanzu haka kasar Sin tana shirin gudanar da aikin bincike kan duniyar wata ta hanyar harba na'urar Chang'e-6, inda za ta samar da damammaki ga sauran kasashen duniya, ta aika da kayayyakin ta zuwa duniyar wata. Duk wadannan sun shaida cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa a bangaren binciken sararin samaniya a sabon zamanin da ake ciki.

Bisa rahoton da hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta fitar, an ce, za a kebe wani wuri na musamman dake cikin na'urar tafiya zuwa sararin samaniya, da kuma na'urar sauka a duniyar wata dake kan na'urar Chang'e-6, domin sauran kasashe su aika da kayayyakinsu zuwa ga duniyar wata. Bisa shirin da aka tsara, za a iya jigilar kayayyaki masu nauyin kilo 10 a cikin na'urar tafiya, haka kuma za a iyar jigilar kayayyaki masu nauyin kilo 10 a cikin na'urar sauka. Kafin wannan wato a ranar 25 ga watan Maris, kasar Sin ta riga ta daddale wata yarjejeniyar hadin gwiwa kan aikin binciken duniyar wata da kasar Faransa. Bisa wannan yarjejeniya, Faransa za ta girke na'urorin gwaji masu nauyin kilo 15 a cikin na'urar Chang'e-6, ciki har da wata kyamara, da kuma wata na'urar tantance sakamakon gwajin da za a samu.

Kasar Sin ta kasance kasa ta uku a duniya, wadda take iya sauke na'urar bincike a duniyar wata ba da garaje ba, kuma kasa daya tak da ke gudanar da bincike a duniyar wata yanzu.

A yanzu haka kasar Sin ta samar da damammakin aikewa da kayayyaki zuwa duniyar wata ga sauran kasashe, lamarin da zai samar da damammaki ga 'yan kimiyya na kasashe daban daban, da su kara samun ilmominsu game da duniyar wata, shi ma wannan sabon hakikanin mataki ne da kasar Sin za ta dauka, yayin da take kokarin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama a bangaren raya aikin binciken sararin samaniya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China