in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba wani dan kasar Sin sarauta a Nijeriya
2019-04-24 14:38:47 cri






A kwanan baya, an gudanar da bikin karramawa a majalisar masarautar Jiwa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya, inda aka ba wani dan kasar Sin sarautar "wakilin ayyuka", saboda gudummawar da ya bayar a fannin inganta hadin gwiwar moriyar juna a tsakanin kasar Sin da Nijeriya da ma raya unguwannin wurin.

Malam Kong Tao shi ne Basinen da aka baiwa wannan sarauta na "wakilin ayyuka". Kong Tao shi ne babban manajan sashen gudanarwa na reshen kamfanin CCECC da ke tarayyar Nijeriya, kuma kawo yanzu ya shafe tsawon shekaru 9 yana aiki a Nijeriya.

Mai martaba Sarkin Jiwa Dr. Idris Musa ya ce, dalilin da ya sa aka karrama malam Kong Tao da sarautar wakilin ayyuka, shi ne yadda shi da kuma kamfanin CCECC suka ba da gudummawa wajen inganta hadin gwiwar Sin da Nijeriya da kuma raya ci gaban Nijeriya a kokarinsu na gina hanyar dogo ta Abuja-Kaduna da ma hanyar dogo ta Abuja wadanda suka ratsa yankin Jiwa. Ya ce, "Malam Kong Tao mutumin kirki ne, a matsayinsa na jagoran sashen kamfanin, ya kulla hulda ta kut da kut da unguwarmu. Kamfanonin kasar Sin sun samar da guraben ayyukan yi a Nijeriya, musamman ga masarautarmu, kuma muna zauna lafiya da su. Mun karrama shi, kuma mun karrama kamfanonin kasar Sin."

Nijeriya ita ce kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma sarakuna sun kasance masu fada a ji a tsakanin al'umma, don haka, babban abin alfahari ne ga mutumin da sarki ya karrama. A cikin 'yan shekarun baya, akwai 'yan kasar Sin da dama a Nijeriya da aka karrama su, abin da kuma ya bayyana yadda al'ummar kasar suka yi na'am da kokarin da kasar Sin take yi wajen raya manyan ayyuka a kasar da kuma cudanyar al'ummomin kasashen biyu..

A hakika, kafin a karrama shi, malam Kong Tao ya kuma taba samun lambobin yabo daga kungiyar injiniyoyi ta Nijeriya da kungiyar kula da harkokin zirga-zirga da sufurin sama ta Abuja da dai sauran hukumomin kasar, baya ga haka, ya kuma ci jarrabawar samun izinin zama injiniya a Nijeriya. Ya ce,"A hakika, fatan mu shi ne, al'ummar kasar su ci gajiya. Misali, hanyoyin dogo da muka gina sun kawo sauyi ga harkokin zirga-zirga a kasar, kuma al'ummar wurin na iya shiga jiragen a farashin da ya dace, don haka sun yi farin ciki sosai. A yayin da muke gina wadannan hanyoyi, mun samar da dimbin guraben ayyukan yi ga mazauna wurin, kuma ba ma kawai ta fannin masu ayyukan kafinta da makamantansu ba, har ma da masu fasahohi. A bara, mun kuma tura gomman 'yan makarantar sakandare na kasar zuwa kasar Sin, don su karo ilmi da fasaha, don haka, mun ba da gudummawa ta fannin raya fasahohi a kasar. Wato ke nan, muna kokarin gina kyakkyawar makoma ga dukkan al'mmomin kasashen biyu baki daya."

Ya zuwa yanzu, Sin da Nijeriya sun cimma dimbin nasarori ta fannin raya manyan ayyuka da ciniki da cudanyar al'umma a tsakaninsu, a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a watan Satumban bara, kasashen biyu sun daddale yarjejeniyar raya shawarar ziri daya da hanya daya cikin hadin gwiwa. A unguwar Jiwa, akwai manyan ayyuka uku da ake gudanarwa, ciki har da hanyar dogo ta Abuja-Kaduna da hanyar dogo ta birnin Abuja da kuma aikin gina sabon zauren jiran fasinjoji na filin saukar jiragen saman Abuja. A game da hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Nijeriya ta fannin raya ziri daya da hanya daya, mai martaba sarki Dr. Idris Musa ya ce,"Kasashen biyu sun cimma nasarorin a zo a gani ta fannin aiwatar da hadin gwiwar bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kuma muna fatan kamfanonin kasar Sin, za su ci gaba da ba da gudummawa, ta yadda za mu samu karin ci gaba ta fannin raya hanyoyin dogo na zamani da ma sauran fannoni." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China