in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan 'yantar da jama'ar Sin za su ci gaba da yin kokarin kafa tsarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma a fannin harkokin teku
2019-04-23 19:56:35 cri

A yau ranar 23 ga wata, rana ce da cika shekaru 70 da kafa sojojin ruwa na rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin. Shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Xi Jinping ya gana da shugabannin tawagogin sojojin kasashen waje dake halartar bikin murnar cika shekaru 70 da kafa rundunar sojojin ruwan 'yantar da jama'ar kasar Sin a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin, inda suka duba jerin kwanon jiragen ruwan sojojin ruwan 'yantar da jama'ar Sin, da jerin kwanon jiragen saman sojojin, da kuma jerin kwanon jiragen ruwan sojojin kasashen waje da suka kai ziyara, kana Xi ya gabatar da kiran kafa tsarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma na bai daya a fannin harkokin teku bisa karko na farko, wanda zai sa kaimi ga bunkasa sojojin ruwan kasar, da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen waje a fannin harkokin teku.

Yyin bikin, gaba daya kasar Sin ta tura jiragen ruwan yaki 32 da jiragen saman yaki 39, ciki har da babban jirgin ruwan yaki mai samfurin Liaoning, da sabon jirgin ruwa dake tafiya a karkashin teku mai amfani da karfin makamashin nukiliya, da sabbin jiragen ruwan yaki da na saman yaki da sauransu, wasu daga cikinsu sun fito a gaban jama'a a karo na farko ne.

Bayan shekaru 70 da suka gabata, sojojin ruwan rundunar sojojin 'yantar da jama'ar Sin sun kasance sojoji masu karfi, da ke iya yin amfani da makamashi daban daban, ciki har da nukiliya, kana suna kwarewa kan fasahohin sadarwa na zamani, da dabarun yaki iri iri. Bikin da aka shirya a wannan karo ya shaida nasarorin da sojojin ruwan kasar Sin suka samu, haka kuma ya nuna cewa, sojojin suna cike da imani yayin da suke kokarin samun ci gaba ba tare da rufa rufa ba.

A matsayinsa na wani na'unin sojoji da suke shan cudanyar da kasa da kasa, sojojin ruwan kasar Sin sun himmatu wajen sauke nauyin da ke wuyansu a cikin shekaru 70 da suka wuce, sa'an nan sun bayar da babbar gudummawa a fannonin kiyaye tsaron tafiye-tafiyen jiragen ruwa na kasashen duniya, da kiyaye oda a kan teku, da ma ba da agaji a kan teku. Kawo yanzu ma dai, gaba daya sojojin ruwan kasar Sin sun tura rukunoni 32 na kiyaye tsaron tafiye-tafiyen jiragen ruwa, da jiragen ruwan yaki 103, da jiragen sama masu saukar ungulu 69 da ma jami'ai da sojoji fiye da dubu 27 domin ba da kariya ga jiragen ruwa na ketare fiye da 6600. A waje daya kuma, jirgin ruwa dake ba da hidimar jinya mai suna "Peace Ark" na sojojin ruwan kasar Sin ta ziyarci kasashe da yankuna 43 a cikin shekaru goma da suka gabata, wanda ya samar da hidimomin jinya ga mutane fiye da dubu 230 daga kasashe daban daban. Duk inda "Peace Ark" yake, ya samu maraba da godiya sosai daga mazauna wurin.

Yayin da shugaba Xi Jinping ke ganawa da tawagogin sojojin ruwan kasashen waje, ya jaddada cewa, sakamakon teku, duniyar da dan Adam ke zama a kai ta hadu, har ma al'ummomin kasashe daban daban suna jin dadin zama da shan wahala tare. A nan gaba, sojojin ruwan kasar Sin za su ci gaba da hada kai tare da sojojin ruwa na kasashe daban daban wajen kiyaye zaman lafiyar teku, da sa kaimi ga bunkasar harkokin teku bisa sabon ra'ayin tsaro na hada kai daga dukkan fannoni don samun dauwamamman ci gaba, ta yadda za a cimma burin raya makomar bil Adama ta bai daya ta fuskar harkokin teku.(Zainab, Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China