Kasar Sin ta wallafa rahoton da ya yi bayani kan ci gaba da gudunmmuwar da aka samu da kuma abubuwan da za a samu nan gaba, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.
An fitar da daftarin, wanda ofishin ayarin dake jagorantar yayata shawarar ya shirya gabanin taro na 2, na hadin gwiwa kan shawarar, wanda za a yi a nan birnin Beijing daga ranar 25 zuwa 27 ga wata.
Ziri Daya da Hanya Daya, shawara ce ta samar da zaman lafiya da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki amma ba kawancen soji ko na yanki ba.
A cewar rahoton, shawarar ba ta bambance kasashe bisa akidunsu, haka kuma ba ta mayar da hankali kan moriyar bangare daya. Kana tana maraba da kasashe su shiga idan suna da muradi. (Fa'iza Mustapha)