An gudanar da taro jiya Lahadi a nan birnin Beijing, don bikin cika shekaru 70 da kafa rundunar sojin ruwa na rundunar 'yantar da al'ummar Sin, wanda ake kafa shi a ranar 23 ga watan Afrilu a shekarar 1949.
Mahalarta taron sun yi bitar yadda rundunar ta faro har ta yi karfi, da takaita ayyukanta na yaki da sauye-sauye da ta fuskanta da shirinta na ko ta kwana, tare da duba makomarta na zama runduna ta zamani da za ta iya gogayya da takwarorinta na kasashen duniya.
Taron ya kuma bayyana yadda rundunar ta samu ci gaba sannu a hankali har ta zama mai karfi kuma ta zamani da za ta iya tsaron iko da iyakoki da muradun kasar Sin.
Ya kara da cewa, rundunar ta fuskanci sauye-sauye kuma ta samu dimbin nasarori tun bayan gudanar da babban taro na 18 na JKS a shekarar 2012.
Har ila yau, an lashi takobin hafsoshi da sojojin ruwa za su bada gudunmuwa wajen gaggauta sauyawa da raya rundunar tare da gina ta zuwa matsayin runduna mai karfi a duniya. (Fa'iza Msutapha)