in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukuncin da WTO ta yanke wa kasar Sin ba nasara ce da wani bangare ya samu ba
2019-04-20 21:37:22 cri

A ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu, kungiyar cinikayya ta kasa da kasa, wato WTO ta sanar da hukuncinta kan karar da kasar Amurka ta gabatar a watan Disamban shekarar 2016 game da matakin da kasar Sin ta dauka na rarraba kaso ga harajin kwastam da ake bugawa kayayyakin alkama da shinkafa da masara da kasar Sin ke shigowa da su daga ketare, inda WTO take ganin cewa, kasar Sin ta dauki mataki ne ba a bayyane ba, kuma ba ta cika alkawarin da ta dauka a lokacin shigarta kungiyar WTO ba. A waje daya, kungiyar WTO ba ta amince da rokon bangaren Amurka ba, wato bangaren Amurka na ganin cewa, bangaren Sin yana da alhakin bayyana yadda yake rabawa da kuma sake rarraba kaso filla filla.

Game da rikice-rikicen cinikayya da a kan tayar tsakanin mambobin kungiyar WTO, a kullum bangaren Sin yana ganin cewa, ya kamata a daidaita su bisa ka'idojin daidaita takkadama na kungiyar kamar yadda ya kamata, kuma ya kamata a mutunta hukuncin da kungiyar WTO ta yanke.

Abin da ya kamata a nuna cewa, kungiyar WTO ta yanke hukunci kan wannan takkadamar cinikin amfanin gona tsakanin kasashen Sin da Amurka, ya alamta cewa, kungiyar WTO tana taka muhimmiyar rawa wajen tsaron ka'idojin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. Sakamakon haka, wannan hukunci ba ya nufin wani bangare ya samu nasara.

Tsarin kasuwanci a karkashin jagorancin hukumar WTO na taka muhimmiyar rawa ga fadada harkokin kasuwanci gami da bunkasa tattalin arziki a duk fadin duniya. Kawo yanzu, adadin yawan kararrakin da aka gabatar ga wannan tsari ya zarce dari biyar, duk da cewa hukuncin da aka yanke ba na tilas ba ne, amma yawancin membobin WTO na maida hankali sosai a kai, wato ko sun samu nasara, ko ba su samu nasara ba, hankalinsu ba zai tashi ba. Wannan na nuna cewa, membobin WTO suna girmama ka'idojin WTO, wato cimma matsaya daya ta hanyar yin shawarwari.

Idan mun dauki kasar Sin tamkar misali, muna iya ganin cewa, zuwa watan Afrilun shekara ta 2018, kasar Sin ta gabatar da kararraki guda 17 ga hukumar WTO, ciki har da guda 8 wadanda aka riga aka yanke musu hukunci. Kana kuma, an yi karar kasar Sin sau 27, ciki har da guda 23 wadanda aka riga aka yankewa hukunci.

Abun da ya kamata a lura da shi, shi ne, yanzu ra'ayin bangare daya da na ba da kariya ga cinikayya da kasar Amurka ke dauka sun kawo mugun tasiri ga tsarin warware takkadama na WTO, musamman ma sakamakon matakan hana shigar da sabbin mambobi cikin hukumar kai kara da Amurka ke dauka, wanda ya haifar da tangarda ga ayyukan wannan bangaren.

Ko shakka babu, akwai bukatar a yi kwaskwarima da kyautata tsarin WTO bisa yanayin da ake ciki, don haka kasashe da dama sun gabatar da shawarwari ko kuma manufofinsu a kai. Ga misalin, kungiyar EU ta bayar da takaitaccen bayani na zamanintar da WTO, a nasu bangaren ma, kasar Amurka da EU da kuma Japan sun bayyana cewa, kamata ya yi a inganta hadin kai tsakanin bangarori guda uku a yayin da ake yin kwaskwarima kan WTO. Kasar Sin ta sanar da manyan manufofinta da abubuwa guda biyar da take tsayawa a kai game da yin kwaskwarima kan WTO a watan Nuwamban bara, wadanda ke tsayawa kan kiyaye tsarin cinikayya na bangarori da dama dake mai da hankali kan dokoki, da adawa da ra'ayin ba da kariyar cinikayya, don taimakawa WTO wajen kara taka rawarta. (Sanusi, Murtala, Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China