in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Sin da Najeriya sun yi sharhi kan hadin-gwiwar kasashen biyu ta fannin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-04-23 10:17:52 cri

A gabannin babban dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya" wanda za'a yi daga ranar 25 zuwa 27 ga wata a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wasu masana harkokin kasa da kasa na Sin da na Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu game da yadda ake tafiyar da ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya" yanzu a Najeriya, gami da makomar hadin-gwiwar kasashen biyu a wannan fanni.

Darektan zartaswa na sashin nazarin harkokin Najeriya na cibiyar nazarin batutuwan Afirka dake jami'ar horas da malamai ta Zhejiang, Michael Ehizuelen ya bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" na inganta mu'amala da cudanya tsakanin kasa da kasa, wadda ta kasance wani sabon salon hadin-gwiwar kasashen duniya mai kawowa juna moriya. Kara hadin kai tare da kasar Sin wajen aiwatar da wannan shawara na da babbar ma'ana ga jamhuriyar tarayyar Najeriya, wadda tattalin arzikinta ke dogaro kusan kacokan kan albarkatun man fetur. Dokta Michael ya ce:

"Gwamnatin Najeriya ta dade tana bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyoyi daban-dabban, tana kuma kokarin horas da kwararru da masana a wasu sabbin fannonin tattalin arziki. Idan har Najeriya ta aiwatar da ayyukan da suka shafi shawarar 'ziri daya da hanya daya', to, za ta iya karfafa hadin-gwiwar tattalin arziki da kasuwanci tare da kasar Sin da sauran kasashe, don samar da mabambantan kasuwanni ga sassa daban-daban a Najeriya. A halin yanzu, ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci na kara yaduwa a duk fadin duniya, kana tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubale da dama, amma dunkulewar duniya waje daya ita ce makomarmu. Don haka ina ganin cewa, shawarar 'ziri daya da hanya daya' na taka muhimmiyar rawa wajen inganta mu'amala tsakanin yankunan duniya daban-daban."

Bana ita ce, shekara ta farko da Najeriya ta shiga cikin shawarar "ziri daya da hanya daya". A nasa bangaren, Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami ne dake koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa a jami'ar Abuja dake Najeriya ya yi tsokaci cewa, an riga an samu nasarori masu yawa a fannin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" a wasu kasashen Afirka, kuma a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki kana kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, ya kamata Najeriya ta kara maida hankali a wannan fanni. Dr. Sheriff Ghali Ibrahim ya ce:

"Idan ka duba za ka ga kasashen Kenya da Djibouti da Masar, tun tuni sun shiga wannan harka, sa'an nan kuma shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kofar ga masu son shiga shawarar a bude take, kuma ko da yaushe za ta zama a bude, duk wanda yake da ainihin ra'ayin kan wannan batu, zai iya shiga a dama da shi. Ita ma Najeriya ta shiga. Mu a Najeriya ka ga wannan shawara ta samar da harkar surufi ta jirgin kasa, musamman ma jirgin da yake zirga-zirga daga Abuja zuwa Kaduna, da wanda zai taso tun daga Lagos har zuwa Kano. Muna fatan cewa Najeriya ta tsunduma tsundun cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya', ya zama cewa shugaba Buhari zai kara habaka shi, da kara duba wurare daban-daban da Najeriya za ta amfana da wannan harka da sauran kasashe wadanda suke kewaye da ita. Sa'an nan ina da yakinin cewa kasashen Afirka suna da wannan tunani iri daya da na Najeriya su ma duk suna so su shiga wannan batu."

Sai dai kuma Dr. Li Wengang, wani masanin harkokin Najeriya daga sashin nazarin batutuwan yammacin Asiya da Afirka na cibiyar nazarin harkokin zaman takewar al'umma ta kasar Sin ya bayyana cewa, kamata ya yi a kara maida hankali kan muhimmancin mu'amalar al'adu yayin da Sin da Najeriya ke hadin-gwiwa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya". Dr. Li ya ce:

"Hakikanin gaskiya, wasu matsaloli sun kunno kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ne saboda rashin fahimtar juna a bangaren al'adu. Ina ganin cewa, ya kamata Sin da Afirka su kara fahimtar juna da samun moriya ta bai daya, saboda mu'amalar al'adu na da matukar muhimmanci. A halin yanzu, akwai daliban kasashen Afirka da dama wadanda ke karatu a kasar Sin, yayin da wasu 'yan kasar Sin ke koyon harsuna da al'adu a kasashen Afirka, al'amarin da zai taimaka matuka wajen kara amincewa tsakanin jama'ar Sin da Afirka." (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China