in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin ruwan kasar Sin na samar da kayayyakin tsaro ga al'ummomin kasa da kasa
2019-04-20 16:49:49 cri

Rundunar sojin ruwa na 'yantar da al'ummar Sinawa, ta ce ta dade tana samar da kayayyakin tsaro ga al'ummomin kasa da kasa tun bayan kafuwarta.

Mataimakin kwamandan rundunar Qiu Yanpeng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai gabanin atisayen sojin ruwa na kasashe daban daban da za a yi domin bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar rundunar sojin ruwan al'ummar kasar Sin.

A cewarsa, rundunar ta kai ziyara sama da 100 zuwa kasashe 94 da gababobin ruwa 138, sannan ta gudanar da horo na hadin gwiwa da kasashe daban daban cikin shekaru 70 da suka gabata.

Ya kara da cewa tun daga shekarar 2010, asibiti mai tafi da gidanka na jirgin ruwan kasar Sin wato Peace Ark, ya je kasashe da yankuna 43 tare da bayar da kulawar lafiya kyauta ga mutane sama da 230,000.

Har ila yau, ya ce cikin sama da kasashe 10 ne za su turo da jiragen ruwa domin faratin da za a yi na bikin cika shekaru 70 da kafa rundunar. Sannan sama da kashe 60 za su tura wakilansu domin halartar atisayen sojin ruwa da za a gudanar domin bikin, kana sama da kasashe 30 za su tura shugabannin rundunoninsu domin halartar bikin.

A ranar 23 ga watan Afrilun ne za a cika shekaru 70 da kafar rundunar sojin ruwa ta 'yantar da al'ummar Sinawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China