in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan aware 31 sun ajiye makamai a yankin Kamaru mai rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi
2019-04-20 15:59:03 cri
Hukumomin a yankin Kamaru dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, sun bayyana a jiya cewa, 'yan aware31 sun ajiye makamansu inda suka shiga shirin sauya hali domin kara shiga al'umma.

Sixtus Gabsa, daraktan kwamitin NDDRC mai kawar da makamai da kwance damarar mayaka da sake shigar da wadanda suka mika wuya cikin al'umma na yankin arewa maso yammacin kasar ne ya bayyana haka a jiya, yayin wani taron bita a garin Bamenda.

Gwamanan yankin Adolphe Lele Lafrique, ya ce yana kira ga jama'a, da su kira sauran wadanda suke dazuka su je cibiyar ta mika wuya, yana mai cewa za a karbe su da hannu bibbiyu tare da ba su horo, sannan ba za a tuhume su da laifin komai ba.

Shugaban kasar Paul Biya ne ya kafa Kwamitin na NDDRC a bara, domin kaucewa amfani da matakai masu tsauri da kuma sa ido da kula da kwance damarar mayaka da sake shigar da tsoffin mayakan Boko Haram da 'yan aware na yankunan arewa maso yamma da kudu maso gabashin kasar cikin al'umma.

Tun cikin watan Nuwamban 2017 ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan aware a yankunan kasar 2 dake da rinjayen masu amfani da Turancin Ingilshi. Masu amfani da Turancin Ingilishi mara rinjaye, a kasar Kamaru dake da masu rinjayen amfani da Faransanci, na kokarin ballewa domin kafa kasar su mai suna "Ambazonia" (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China