in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 7 sun mutu sanadiyyar harin da Boko Haram ta kai yankin arewa mai nisa na Kamaru
2019-04-20 15:37:11 cri
A kalla mutane 7 ne suka mutu, yayin da wasu 5 suka samu munanan raunuka, sanadiyyar wani hari da Kungiyar Boko Haram ta kai Tchakarmari na yankin Mayo-Sava dake yankin arewa mai nisa na Kamaru, a ranar Alhamis da daddare.

Gwamnan yankin arewa mai nisa, Midjiyawa Bakary, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, da tsakar daren ranar Alhamis ne mayakan Boko Haram suka kai hari yankin kan babura da motocin pick-up. Ya ce mutane 7 sun mutu, da suka hada da mata 2 da maza 5, sannan mayakan sun sace tumaki tare da kona gidaje. Baya ga haka, ya ce wasu mutane 5 sun samu munanan raunuka, inda kawo yanzu wasu daga cikinsu, suka fita daga matakin hadari.

Ya ce hare-hare kan karu a birane da kauyukan yankin arewa mai nisa a irin wannan lokaci da watan Ramdana ke karatowa, a don haka ya yi kira ga mutane su kara yin taka tsan-tsan.

Rahotanni na bada bayanai daban-daban game da adadin wadanda suka mutu. Inda wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta daga Kamaru, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a kalla fararen hula 9 ne mayakan Boko Haram suka kashe, yayin da wasu mazauna yankin da suma suka bukaci a sakaya sunayensu, suka shaidawa Xinhua cewa, mutane 11 ne suka mutu, ciki har da yara 3. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China