in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
6.4%! Tattalin arzikin kasar Sin ya nuna alama mai yakini
2019-04-17 20:57:03 cri
Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar na nuna cewa, a cikin watanni uku na farkon bana, yawan kudin da kasar ta samu daga sarrafa dukiyar kasa (GDP) ya kai RMB triliyan 21.3433, wato ya karu da kashi 6.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, kuma saurin karuwarsa ya yi daidai da na watanni uku na karshen shekarar bara. Baya ga haka, alkaluman da aka fitar a fannonin samun guraban ayyukan yi, farashin kaya, yawan kudin shiga da dai sauransu sun ma sun wuce alkaluman da ake fatan samu. Wannan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya fara ingantuwa, lamarin da ba kawai ya farfado da imanin kasuwa ba, har ma ya aza harsashi mai kyau na cimma burin bunkasuwar tattalin arziki a bana.

A zahiri, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin a farkon watanni ukun bana na da wasu siffofi uku na musamman:

Na farko, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata. Saurin karuwar tattalin arzikin kasar ya kai kashi 6.4 bisa dari a farkon watanni uku na bana, wanda ya cimma burin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, wato tsakanin kashi 6 zuwa 6.5 bisa dari, ya kuma zarce kwarya-kwaryar hasashen da asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi na kashi 6.3 bisa dari. Har wa yau, daga watan Janairu zuwa Maris din bana, an kara samun mutane miliyan 3.24 wadanda suka samu ayyukan yi a birane da garuruwan kasar Sin, wanda ya dauki kashi 29.5 bisa dari na burin da aka tsara a duk shekara. Duk wadannan manyan alkaluman tattalin arzikin kasa sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba har ma ya samu farfadowa. Na biyu kuwa, tsarin tattalin arzikin ya kara samun kyautatuwa. Na uku, wato jama'a na kara nuna imani ga makomar tattalin arzikin kasar Sin.

A yayin da ake kara fuskantar takaddamar ciniki da kuma rashin tabbas a fannin ci gaban tattalin arziki, nasarorin da kasar ta Sin ta samu a tattalin arzikinta gaskiya ba abu mai sauki ba, nasarorin da kuma suka bayyana yadda tattalin arzikin kasar ya jure takaddamar ciniki, wadanda kuma suka aza harsashi ga ingantuwar tattalin arzikin kasar. A wani bangare kuma, hakan sakamako ne da aka samu daga manufar yin gyare-gyare da bude kofa da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, wanda kuma ya bayyana imanin kasa da kasa ga kasuwar kasar Sin.

Kasancewarta kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, ingantuwar tattalin arzikin kasar babu shakka wani albishir ne ga duniya baki daya. A hasashen tattalin arzikin duniya na baya-bayan da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar, ya rage karuwar ci gaban tattalin arzikin duniya, a yayin da ya daga saurin bunkasuwar kasar Sin, hasashen da ya shaida yadda kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar jagora a bunkasuwar tattalin arzikin duniya.(Masu fassara: Bilkisu, Murtala, Lubabatu, dukkan ma'aikatan sashen Hausa)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China