Shugaba Xi ya ce, Notre-Dame wata muhimmiyar alama ce ta wayewar kan kasar Faransa kana babbar albarkar wayin kan bil-Adama.
Kamar Faransawa, al'ummar Sinawa ma sun kadu matuka da bala'in gobarar. Ya ce, kasar Sin ta yi imanin cewa, za a gudanar da aikin gyara majami'ar yadda ya kamata, kuma za a sake dawo da kimarta bisa kokarin al'ummar Faransa tare da goyon bayan al'ummomin kasashen duniya.(Ibrahim)