in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanoni da dama daga kasashen shawarar ziri daya da hanya daya sun halarci bikin kasuwanci na canton fair
2019-04-15 21:26:32 cri
A yau Litinin ne, a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, aka bude bikin kasuwancin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 125, wato "Canton Fair", Rahotanni na cewa, fiye da rabin kamfanoni dake halartar bikin, sun fito ne daga kasashe da yankunan dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar.

Mai magana da yawun bikin Xu Bing ya bayyana cewa, wadannan sun hada da kamfanoni 383 daga kasashe da yankuna 21 dake cikin shawarar ta ziri daya da hanya daya, ciki har da kasashen Rasha, da Poland da Philippines da Isra'ila.

Haka kuma bikin, ya sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanoni da hukumomin kasuwanci daga kasashe da yankuna 33 dake cikin shawarar. Bikin yana fatan kulla alaka da dukkan kasashe da yankunan cikin shekaru biyu ko uku.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China