in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya da Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram 27
2019-04-15 19:59:09 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa, dakarunta da na kasar Kamaru, sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 27, a wani sabon hari da suka kaddamar da nufin kawar da gyauron mayakan a kan iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru. Baya ga tarin makamai da albarusai da aka kwato da kuma bindigogin mayakan da dakarun kasashen biyu suka lalata.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Sagir Musa, ya ce, sojojin sun yi dauki ba dadi da mayakan ne a yankin arewacin kauyukan Wulgo, Tumbuma, da Chikun Gudu da Bukar Maryam, dukkansu a bangaren Najeriya.

Sai dai Musa ya ce, babu wani sojin da ya rasa ransa daga bangaren kasashen biyu. A cewarsa, ana ci gaba da kai hare-haren hadin gwiwa, musamman a yankin Gombaru-Ngala da yankunan dake kawaye da shi, domin yakar mayakan da suka arcewa barin wutar da dakarun hadakar kasashen Najeriya da Benin da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar ke yi kan mayakan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China