in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe 'yan aware 3 da sojoji 4 a yankin Kamaru mai fama da tashin hankali
2019-04-15 19:58:23 cri
Rahotanni daga kasar kamaru na cewa, an kashe a kalla 'yan aware masu dauke da makamai guda uku da sojojin gwamnati hudu jiya Lahadi da dare, a wani arbatu da ya barke a Bali, wani kauye a yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru, daya daga cikin yankuna biyu na kasar da ake magana da Turancin Ingilishi mai fama da tashin hankali.

Dakarun gwamnati da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya zanta da su, sun tabbatar da faruwar arangamar, tare da jaddada cewa, wata tawaga tana can na ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Sai dai sakataren watsa labaran 'yan awaren Cris Anu, ya aike da sakon murya ranar Lahadin da ta gabata a shafinsa na WhatAspp, yana mai gargadin cewa, yankin na cikin hadari. Don haka, ya bukaci mazauna Bali, da su fice daga yankin don tsira da rayukansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China