Wang Zhigang ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci a yayin da ake yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha shi ne hadin gwiwar kwararru, a halin yanzu Sin ta fi son neman kwararru bisa lokacin baya. Ya ce a shekarun baya baya nan, Sin ta gudanar da manufofin sa kaimi ga shigo da kwararru, da sassauta sharudan bada iznin zama da aiki ga 'yan kasashen waje, da samar da sauki gare su, da kuma warware matsalolin bada tabbaci ga rayuwarsu, da iznin zama, da samar da ilmi ga yaransu da sauransu.
Sin tana kokarin yin musayar kimiyya da fasaha a tsakaninta da sauran kasashen duniya a wadannan shekaru, da kafa dandalin hadin gwiwa na yin kirkire-kirkire don samun moriyar juna cikin adalci. (Zainab)