190417-An-kafa-cibiyar-nazarin-harkokin-Sin-da-Afirka.m4a
|
Ranar Talata 9 ga watan Afrilun shekarar 2019 ne, aka gudanar da muhimmin taron kafa cibiyar nazarin dangantakar kasashen Sin da Afrika a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.
Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma darektan ofishin kwamitin harkokin waje na kwamitin tsakiya na JKS ya halarci bikin kafa cibiyar, tare da karanta wasikar shugaba Xi Jinping ta murnar kafa cibiyar, inda ya ce, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya kana nahiyar Afrika shiyya ce dake kunshe da mafi yawan kasashe masu tasowa a duniya
An kafa cibiyar ce, domin nazarin muhimman bangarorin da suka shafi tsarin shugabanci da raya ci gaban kasashen Sin da Afrika.
Kafa cibiyar, ya biyo bayan muhimman kudurori 8 wadanda shugaba Xi Jinping ya gabatar a lokacin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a Beijing 2018, kuma batun kafa cibiyar na daya daga cikin kudurorin guda 8 da shugaba Xi ya ambata
Farfesa Sarah Anyang Agbor kwamishiniyar hukumar kula da ci gaban kimiyya da fasaha ta kungiyar tarayyar Afrika AU wadda ta gabatar da jawabi a madadin shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana abin da ta kira, karamcin da kasar Sin da al'ummar Sinawa ke nunawa kasashen Afrika.
Tsohon shugaban kasar Mozambique Joaqium Albertor Chissano, ya bayyana cewa, kafa cibiyar wani sabon mataki ne na karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika wanda zai taimakawa matasa da kwararrun masanan kasashen biyu wajen bunkasa moriyar al'ummomin kasashen biyu wato Sin da Afrika.
A cewarsa, kafa cibiyar wani muhimmin tubali ne da zai kara kyautata mu'amalar tsakanin al'ummomin sassan biyu tare da samar da kyakkyawar makoma ga bil Adama musamman wajen raya ci gaban kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire da kuma samun moriya ga jama'ar kasashen Sin da Afrika.
Sama da wakilan gwamnatoci, kwararru, jami'an diplomasiyya na kasashen Afrika sama da 40 ne suka halarci bikin kaddamar da cibiyar. (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)