in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na taka muhimmiyar rawar tabbatar da bunkasar ciniki tsakanin kasa da kasa
2019-04-12 20:35:42 cri

Bisa alkaluman cinikin waje da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a yau Juma'a, a cikin farkon rubu'in bana, jimillar cinikin waje da kasar Sin ta yi ya kai kudin Sin yuan triliyan 7.01, wato adadin ya karu da kaso 3.7%, bisa kwatankwancin adadin na bara.

A lokacin da saurin karuwar cinikin waje da ake yi tsakanin kasa da kasa yake raguwa sakamakon hali mai tsanani da cinikin waje tsakanin kasa da kasa ke ciki, ba abu ne mai sauki ba ga kasar Sin da ta samu wannan kyakkyawan sakamako a wannan farkon rubu'i na bana. Wannan sakamako ya sake alamta cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya yiya jure wahala sosai., har ma za a iya samu karin damamaki a kasuwar kasar Sin.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, a cikin farkon rubu'in bana, a lokacin da kasar Sin take kokarin bunkasa cinikin waje ba tare da tangarda ba, take kuma mai da hankali kan inganta cinikin. Daga bangarori uku ne za a iya ganin wannan halin da ake ciki.

Da farko dai, abokan cinikayyanta, wadanda suka fito daga sassa daban daban na duniya sun karu. Alal misali, a cikin farkon rubu'in bana, ko da yake yawan cinikin da aka yi tsakanin kasashen Sin da Amurka ya ragu da kaso 11%, a bayyane take cewa yawan ciniki da aka yi tsakanin kasar Sin da sauran muhimman abokan cinikayya, kamar su kasashen Turai da na kudu maso gabashin Asiya, da Japan, da kuma kasashe wadanda suke da sha'awar "ziri daya da hanya daya" ya karu sosai. Sannan, yawan shige da fice da aka yi tsakanin kasar Sin da kasshen Latin Amurka, ko kuma tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya samu karuwa. Sakamakon karuwar abokan cinikayya, an rage hasarar da kasar Sin ta samu sakamakon takkadamar cinikayya da ke kasancewa tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, har ma karfin nata na tinkarar hadari ya karfafu.

Na biyu shi ne an kyautata tsarin da ake bi wajen fitar da kayayyaki zuwa ketare. Kasar Sin ta fitar da karin wasu kayayyaki masu daraja, wadanda suka hada da kayayyakin injuna da lantarki, da na'urorin sarrafa kayayyaki. Wannan ya nuna yadda kayayyakin kirar kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa. A fannin shigo da kaya kuma, an shigo da karin na'urorin ayyukan likitanci, da wasu injuna cikin kasar Sin a farkon rubu'in bana, inda karuwarsu ta kai kaso 10.5, da kaso 10.8 bisa dari. Hakan ya nuna yadda Sinawa ke kara sayen wasu kayayyaki masu daraja.

Na uku shi ne yadda kasar ke samun karuwa sosai a fannin cinikin kasa da kasa. Hakika ci gaban tattalin arzikin cikin gidan kasar Sin, ya taka muhimmiyar rawa wajen raya aikin ciniki da kasashen waje.

Idan ba mu manta ba, kungiyar ciniki ta duniya WTO, ta rage hasashenta kan karuwar cinikin kasa da kasa na bana, daga kashi 3.7% zuwa 2.6% a wasu kwanaki 10 da suka wuce, jimillar da ta zama mafi kankanta cikin shekaru ukun da suka wuce. Sa'an nan dalilin da ya sa aka rage hasashen, shi ne domin takaddamar ciniki da ake fama da ita, gami da tsanantar yanayin rashin tabbas ga tattalin arzikin duniya. Ta yi la'akari da wannan yanayin da ake ciki, yadda kasar Sin ta kiyaye yanayin ayyukan shigi da fice, tare da samun karuwa cikin kima, wannan ba wani abu mai sauki ba ne.

Wannan nasara a wani bangare ta nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya iya jure wahala sosai. Ko kadan bai raunana ba a gaban kalubalen takaddamar ciniki, har ma an mai dai wannan kalubale ya zama wata dama.

Saboda haka, asusun lamunin duniya IMF ya kara hasashen da ya yi kan karuwar tattalin arziki a shekarar 2019 zuwa kashi 6.3%, jimillar da ta karu da kaso 0.1 idan an kwatanta da hasashen da ya yi a wajen Janairun bana. Ma iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin dake rika samun karuwa, ya zama wani ginshikin da ya tabbatar da karuwar cinikinta da kasashen waje.

A wani bangare na daban kuma, bayan da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da muhimman matakai guda 4 na kara bude kofar Sin ga ketare, a yayin taron dandalin tattaunawar Asiya na Boao a lardin Hainan a shekarar bara, wato sassauta kayyade ba da iznin shiga kasuwar kasar Sin, da kyautata yanayin zuba jari domin kara shigar da jarin waje, da kara karfin kiyaye aikin mallakar fasaha, da kara shigar da kaya kasar, an fara daukar matakai masu nasaba da hakan daya bayan daya, wadanda suka karfafa gwiwar kamfanonin aikin shige da fice, da kuma samar da kyakkyawan yanayi wajen raya cinikin waje. Kamar yadda Chad Bown,, kwararre a fannin ilmin ciniki a cibiyar nazarin tattalin arzikin duniya ta Peterson ta kasar Amurka ya fada, yadda kasar Sin take kara bude kofarta ga ketare, yana taimaka wajen sassauta matsalar ciniki da ake fuskanta a duniya.

A matsayinta na rukuni na biyu mai ci gaban tattalin arziki, kasar Sin tana raya cinikin waje yadda ya kamata, duk da rashin tabbaci da ake fuskanta ta fuskar cinikin kasa da kasa a halin yanzu. Hakan ya nuna kyakkyawar alama, da kuma karfafa gwiwar kasashen duniya ta fuskar ciniki. Nan ba da dadewa ba, za a yi taron dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" tsakanin manyan jami'ai karo na 2 a birnin Beijing, kana kuma za a gudanar da taron baje kolin kayayyakin shifi na duniya na kasar Sin karo na 2 a karshen shekarar bana, lamarin da zai kara samar da zarafi wajen bunkasa cinikin kasa da kasa. Kasar Sin kuma za ta ci gaba da taka rawarta, wajen yin cinikin duniya yadda ya kamata. (Sanusi Chen, Bello Wang, Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China