Yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce a yanzu, ma'aikatar ta tantance sabbin ayyukan yankunan, wanda za a fitar ga al'umma a lokacin da ya dace.
Ya ce tun bayan kafa yankin ciniki cikin 'yanci na gwaji na farko a Shanghai a shekarar 2013, Kasar Sin ta kafa irin wadannan yankuna guda 12, wadanda suka haifar da nasarori guda 153 da aka yi koyi da su a sassan kasar.
Kakakin ya ce irin wadannan ayyukan, sun taka muhimmiyar rawa wajen saukaka matsin da kamfanoni ke fuskanta da kara karfafa harkokin kasuwanni da inganta muhallin kasuwanci da yayata alfanun da aka samu daga manufar bude kofa da gyare-gyare. (Fa'iza Mustapha)