in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu babban sakamakon yaki da talauci a kauyen Nanwendu na lardin Hebei na Sin
2019-04-12 11:02:33 cri

Bana shekaru 70 ke nan da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, al'ummun kasar sun himmatu karkashin jagorancin jam'iyyar kwamnis ta kasar Sin, inda suka samu manyan sakamako a fannoni daban daban, musamman ma aikin yaki da talauci, a yau za mu yi mako muku bayani game da kokarin da ake domin kubutar mazauna kauyen Nanwendu na gundumar Pingshan ta lardin Hebei na kasar Sin daga kangin talauci.

Ya zuwa karshen shekarar 2018 da ta gabata, manoman kauyen Nanwendu da yawansu ya kai sama da iyalai 200 sun cimma burin kubutar da kansu daga kangin talauci, lokacin da wakilinmu ya ziyarci kauyen, ya ga tituna masu fadi da wurin da aka kebe domin kiwon kifaye da kuma filin nune-nunen al'adun kauye mai kyan gani, ko ina ana iya ganin itatuwa masu launin kore.

Dattijo Fan Gengshun, mai shekaru 93 da haihuwa yana zaune a kan wata kujera yana shan mai dumin hasken rana, ya gaya mana cewa, yana jin dadin rayuwa matuka, a cewarsa: "Dakin da nake kwana da aibincin da nake ci duk suna da inganci, ina jin dadi matuka, abn dake kara faranta min rai shi ne, a halin yanzu muhallin kauyenmu yana kara kyautatwa, kusan ma babu sauro a nan, ga dakina da kayayyakin dake cikin gidana, kusan iri daya ne da wadanda mazauna birane suke amfani da su."

Gaba daya akwai iyalai 204 a cikin kauyen Nanwendu, adadin manoman kauyen ya kai 687, daga zuriya zuwa zuriya suna noma a gonaki, shekaru 3 da suka gabata, kaso 1 bisa 3 na manoma suna fama da kangin talauci, daga baya tawagar yaki da talauci ta hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta birnin Shijiazhuang ta zo kauyen domin taimaka musu, ta yadda za su kubuta daga yanayin fama da talauci, sakataren farko na kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Zhang Duanshu ya tuna cewa, "A wancan lokaci, manoman kauyen suna noman ne a gonaki kawai, kusan babu kudin shiga, kullum suna zama ne a gida, babu wani aiki, yanayin kauyen shi ma ba shi da tsabta, ga dati ta ko'ima a gefen titin tabo."

Sai dai Zhang Duanshu ya je gidajen manoma tare da abokan aikinsa na tawagar yaki da talauci domin ya binciki hakikanin yanayin da suke ciki, da kuma dalilan da suka jefa su cikin mawuyancin yanayin kangin talauci, a karshe dai sun tsai da kuduri cewa, za su yi kokarin samun jarin da za a zuba, tare kuma da yin amfani da albarkatun gonaki da tsaunukan kauyen domin kubutar da manoman daga kangin talauci.

Kauyen Nanwendu yana kusa da ni'imtaccen wurin Xibaipo mai matsayin koli a kasar, inda aka taba gudanar da juyin-juya hali kafin kafuwar sabuwar kasar Sin, bayan kokarin da ake, nan da nan kamfanin raya aikin gona na Baisheng na lardin Hebei ya fara zuba jari a kauyen domin gina aikin yawon shakatawa ta hanyar nuna aikin gona na zamani, jagoran kamfanin Yang Guang ya yi mana bayani cewa, "Gaba daya adadin jarin da kamfaninmu ya zuba a kauyen ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan 178, a halin da ake ciki yanzu, mun yi hayar kusan hekta 350 na gonakin kauyen, mun shukka 'ya'yan itatuwa iri daban daban a gonakin, muna kuma bukatar ma'aikata da yawa a lokacin da ake girbin 'ya'yan itatuwa bayan sun girma."

Ya zuwa karshen shekarar 2018, an dasa itatuwan tuffa da inabi a gonaki mai fadin muraba'in mita 3000, kuma an gyara kogunan dake kusa da kauyen, kana an gina gada da titi da wurin adana giya a kauyen, daga nan an kammala matakin farko na aikin samar da wurin yawon shakatawan gonaki na zamani a kauyen.

Fan Chunxi, manomin kauyen mai shekaru 49 da haihuwa ya taba fama da talauci mai tsanani, saboda matarsa ba ta da lafiya, ba zai yiyu ba ya je aiki a waje, shi ya sa kusan ba shi da kudin shiga, amma yanzu yana aikin shara da kuma kashe gobara a kauyen, yana mai cewa, "Yanzu kudin shigar da nake samu a kowane wata ya kai yuan 1800, kuma ina ba da hayar gonan gidana ga wasu, kana zan iya samun karin riba daga kamfanin kauyen, gaba daya kudin shigar da nake samu a ko wace shekara ya kai sama da dubu 20."

Sakataren farko na kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Zhang Duanshu ya bayyana cewa, nan gaba za a kara himmatu kan aikin yawon shakatawa a kauyen domin samar da karin wadata ga manoman kauyen Nanwendu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China