in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na ci gaba da kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2019-04-11 19:39:25 cri

Adadin kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta kaddamar jiya Laraba 10 ga wata ya nuna cewa, alkaluman sayayya wato CPI na kasar Sin a watan Maris ya ragu da kashi 0.4 cikin dari bisa na watan Febrairu, kuma ya karu da kashi 2.3 cikin dari, bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Alkaluman CPI bai sauya ba.

Kana kuma Alkaluman samar da kayayyaki wato PPI a watan Maris ya karu da kashi 0.1 cikin dari bisa na watan Febrairu, kuma ya karu da kashi 0.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Alkaluman PPI karuwa yake yi. A ranar Talata ne asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF ya kara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kashi 6.3 cikin dari a shekarar 2019 a cikin sabon rahotonsa, wanda ya karu da kashi 0.1 cikin dari bisa yadda ya yi hasashe a wata Janairun bana. Sabo da haka kasar Sin ta zama kasa daya tak, da IMF ya kara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arziki a duniya.

Da wuya sosai kasar Sin ta samu irin wannan ci gaba. A cikin sabon rahoton IMF kan hasashen tattalin arzikin duniya, IMF ya rage hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 3.3 cikin dari a shekarar 2019, amma hasashen ya nuna a watan Janairun shi ne kashi 3.5 cikin dari. IMF ya ce, a bana, rukunonin tattalin arzikin duniya da yawansu ya kai kashi 70 cikin dari ne za su fuskanci raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu. A daidai wannan lokaci, tattalin arzikin kasar Sin ya samu karuwa. Wasu batutuwa suna kara taimakawa wajen raya tattalin arziki ba tare da tangarda ba, musamman ma bukatun cikin gida sun karu sosai, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba tare da tangarda ba.

Tun daga bara, kasar Sin ta dauki jerin matakai na zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar, gami da kara bude kofarta ga kasashen waje. Wadannan matakai sun hada da rage haraji, da kudin da ake karba don rage nauyin dake kan kamfanoni da 'yan kasuwa, da sassanta sharadin da aka shata ma kamfanoni masu neman shiga wata kasuwa don kyautata muhallin gudanar da ciniki, da daukar matakin hukunta masu keta hakkin mallakar fasahohi ta hanyar ci musu tara, don karfafa aikin kare hakkin, da kayyade a cikin dokar zuba jari ta 'yan kasuwa baki cewa za a ba kamfanoni na gida da na waje ikon iri daya, lamarin da ya sa yawan kudin cinikin da aka kulla wajen bikin Expo na kayayyakin da aka shigar da su daga ketare na farko a kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 57.83. Ta wadannan matakai, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka na ci gaban da kokarin gyare-gyare a gidanta gami da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda aka karfafa wa kamfanonin gida da waje gwiwarsu, da sa kaimi ga tattalin arzikin kasar Sin, don ya rika samun ci gaba cikin kima.

Wasu alkaluman da aka samu sun nuna cewa, cikin shekarar 2018 kasar Sin ta yi amfani da jarin kasashen waje da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 134.97, adadin da ya karu da kashi 3% bisa na shekarar 2017, haka kuma ya cimma wani matsayin da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Sa'an nan a fannin zuba jari ga kasuwannin ketare, kasar Sin ta zuba kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 130, jamillar da ta sa ta zama kan gaba a duniya a wannan fanni. Shugaban kamfanin Apple na kasar Amurka Timothy Cook ya taba bayyana cewa, manufar kasar Sin ta bude kofa na taka muhimmiyar rawa ga yunkurin samun walwalar duniya, inda ya ce "Mun gode kasar Sin kan yadda ta bude kofarta, ta ba mu damar zama daya daga cikin iyalinta."

Asusun ba da lamuni IMF ta kimanta a kwanan baya, cewar tattalin arzikin kasar Sin zai karu da 6.3% a shekarar 2019. Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, tattalin arzikin kasar zai karu da 6% zuwa 6.5% a shekarar da muke ciki. Yaya za a gano hakikanin ma'anar wannan burin da kasar Sin take kokarin cimmawa? A bangare daya, kasar Sin ta kasance kamar kungiyar tattalin arziki mafi karfi ta biyu a duk duniya, wato yawan GDP da ta yi a shekarar 2018 ya kai fiye da kudin Sin yuan triliyan 90, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 13 da wani abu. Kamar yadda Mr. Zhang Tao, mataimakin babban direktar IMF ya ce, idan tattalin arzikin kasar Sin zai karu da 6.3% a shekarar 2019 kamar yadda ake fata, tabbas ne yawan tattalin arzikin kasar zai karu zai kai wani sabon matsayi a tarihi. A waje daya kuma, a cikin kasashe biyar mafi karfin tattalin arziki a duniya, saurin karuwar kaso 6.3% da tattalin arzikin kasar Sin zai karu, da kuma asusun ba da lamuni ta IMF ta kimanta ya fi yawa, wannan ya alamta cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zama a kan mukamin shugabanci a cikin kasashe 5 mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma za ta ci gaba da kasancewa kamar wani muhimmin injin dake taka muhimmiya rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duk duniya gaba daya.

A halin da ake ciki yanzu, bil Adama na fuskantar babban sauyin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru dari da suka gabata, sannan yana da sabuwar damar gyaran fuskokin masana'antu da sana'o'i daban daban, amma a waje daya, ana fuskantar hadura da kuma kalubaloli iri iri, kamar su rashin karfin farfadowar tattalin arzikin duniya, da ra'ayoyin ba da kariyar cinikayya, da kuma matakan da wasu suke dauka da kansu kadai. Kamar yadda aka yi kira a cikin rahoton "Hangen nesa kan tattalin arzikin duniya" da IMF ta fitar, an ce, ya kamata kowace kasa ta dauki matakan ingiza bunkasar tattalin arziki da za su yi daidai da halin da take ciki, da kuma tabbatar da ganin matakan da za su dauka sun bayar da gudummawa ga bunkasar tattalin arziki. Bugu da kari, dole ne a hanzarta kawar da sabanin da suke kasancewa kan batun cinikin waje, ta yadda za a iya karfafa gwiwar masu zuba jari da masu sayayya baki daya. (Tasallah, Bello, Sanusi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China