in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na ta da hankali a yankin Gabas na tsakiya, da ma sauran sassan duniya
2019-04-09 20:46:02 cri

A 'yan kwanakin nan, yankin Gabas na tsakiya ya shiga wani hali, har ma irin wannan hali ya tsananta sakamakon matakan da kasar Amurka ta yi ta dauka a yankin.

A ran 9 ga watan Afrilu, an fara zaben 'yan majalisar dokokin kasar Isra'ila. A 'yan kwanakin baya, shugaba Donald Trump na Amurka ya yi shelar cewa, kasar Isra'ila tana da ikon mulkin tudun Golan. Kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa bi da bi ne suka zargi wannan kuduri na Amurka da kakkausar murya. Amma, kusan a lokaci daya, a jiya Litinin, shugaba Donald Trump na Amurka ya shelanta cewa, kasarsa ta mai da rundunar juyin juya hali ta Musulunci ta kasar Iran a matsayin kungiyar ta'addanci.

Wannan ne karo na farko da kasar Amurka ta mai da rundunar sojan wata kasa mai cikakken ikon mulkin kai a matsayin wata kungiyar ta'addanci. Wadannan muhimman al'amura biyu sun bayyana cewa, kasar Amurka, tana canja manufarta kan yankin Gabas na tsakiya, matakin da ita kanta ta dauka na kawo barazana ga zaman lafiyar duniya gaba daya.

Da farko dai, game da tudun Golan. A ran 25 ga watan Maris, a fadar White House ta Amurka, Donald Trump, da Benjamin Netanyahu wanda ya yi ziyara a kasar Amurka, sun kulla wata yarjejeniya, inda suka shelanta cewa, kasar Amurka ta amincewa kasar Isra'ila ta yi iko da tudun Golan. Kamar yadda kasashen duniya suka yi a lokacin da kasar Amurka ta ce ta dauke ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus, a wannan karo ma, kasashen duniya sun nuna adawa da wannan kuduri na kasar Amurka gaba daya, babu wata kasa ta daban da ta nuna goyon bayan matakin, kana babu wata kasa daban da ta dauki mataki irin na ba-ruwanmu.

A ran 27 ga watan Maris, kwamitin sulhun MDD ya kira wani taron gaggawa. A yayin taron, a cikin kasashe 15 na mambobin dindindin, da wadanda ba na dindindin ba a kwamitin, ban da kasar Amurka ita kanta, sauran kasashe 14 dukkansu sun nuna adawa da matakin da kasar Amurka ta dauka.

Dalilin da ya sa kasar Amurka ta sabawa ra'ayi na kasashen duniya wajen nuna goyon baya ga Isra'ila don ta mallaki yankin tudu na Golan, da kara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, shi ne domin kasar ta canza manufarta game da yankin.

Tun bayan da Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka, 'yan siyasan kasar masu son daukar matakan nuna karfin tuwo suka fara zama masu fada a ji, musamman ma a fannin tsara manufofi masu alaka da yankin Gabas ta Tsakiya. Yanzu haka kasar Isra'ila ta kara samun karfin soja, sa'an nan tana ta matsa wa bangaren Falasdinu lamba. Ganin haka ya sa kasar Amurka ta yi watsi da manufar neman sulhu tsakanin Isra'ila da Falasdinu, sa'an nan ta dauki manufar taimakawa Isra'ila, gami da kebance kasar Iran.

Yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, kasar Iran na samar da karin tasiri ga sauran kasashe, lamarin da ya sanya kasar Amurka damuwa sosai. Wani rahoton aikin tsaro da kasar Amurka ta gabatar, ya nuna yadda kasar Iran ke da alakar kut-da-kut tare da kungiyar Hizballah dake kasashen Syria, Iraki, da kuma Lebanon, gami da dakarun Hamas dake Zirin Gaza.

A ganin gwamnatin kasar Amurka, kasar Iran da wadannan kungiyoyi, suna kokarin kafa wani kawance ne na masu bin mazhabar Shi'a, wanda zai yi wa kasar Isra'ila zobe, gami da haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka. Saboda haka, kasar Amurka tana kallon kasar Iran a matsayin wata babbar abokiyar gaba. Sa'an nan yadda kasar Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliya ta kasar Iran, gami da sake kakabawa kasar takunkumi, ya nuna yunkurinta na dakile kasar Iran.

Bisa wannan yunkuri ne, gwamnatin Trump ta sanar da sanya rundunar sojojin kasar Iran ta IRG, wato (Islamic Revolutionary Guard) cikin jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci. Matakin da kasar Amurka ta dauka ya nuna yadda kasar ta tsaurara takunkumin da ta sanya wa kasar ta Iran. Cikin sanarwarsa, shugaba Trump ya ce wannan mataki zai baiwa kasarsa damar matsawa kasar Iran lamba mai tsanani matuka, wanda hakan zai shafi karin fannoni daban daban. Yanzu haka duk wani mutum da ya yi ciniki da rundunar sojojin kasar Iran, ko kuma rufa musu baya, zai fuskanci hadura sosai.

Mai da rundunar sojan wata kasa mai cikakken mulkin kai a matsayin wata kungiyar 'yan ta'adda, abu ne wanda da kyar ake ganinsa a duk fadin duniya, kuma abun da Amurka ta yi ya riga ya fusata Iran kwarai da gaske, har ma akwai yiwuwar barkewar tashe-tashen hankula a wannan yanki. Iran ta yi Allah wadai da abun da Amurka ta yi, inda a cikin wata sanarwar da ta bayar, kwamitin koli mai kula da harkokin tsaron Iran ya nuna cewa, abun da Amurka ta yi na da hadarin gaske kuma ba bisa doka yake ba, ya kuma sanar da ayyana babban ofishin bada umurni ga harkokin soja na Amurka wato United States Central Command, gami da sojojin da ya girke a yammacin Asiya a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Ana iya ganin cewa, ja-in-ja tsakanin Amurka da Iran zai kara tsananta, kuma Amurka za ta kara samar da goyon-baya ga Isra'ila a harkokin yanki da na soja.

Yake-yaken da Amurka ta yi a Afghanistan da Iraki, ba kawai sun jawo matsaloli da yawa ga Amurka ita kanta ba ne, har ma hakan ya haifar da matsaloli, da barazana sosai ga makomar yankin Gabas ta Tsakiya, al'amarin da ya kawo tsaiko ga zaman lafiya da ci gaba a wannan yanki. Yanzu, Amurka ta yi biris da dokoki, gami da ka'idojin kasa da kasa, da daukar mataki a gefe guda, har ma ta jawo tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya, abun da ya jawo koma-baya ga tarihi, kana barazana ce ga zaman lafiya.

Yankin Gabas ta Tsakiya ya sha jin radadin yake-yake, kuma jama'arsa na matukar son zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma ita Amurka ta yi wannan abun da bai dace ba. Shin ko ina za'a kwana game da makomar yankin? (Sanusi Chen, Bello Wang, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China