in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya aika da sakon murnar kafa cibiyar nazarin kasashen Sin da Afrika
2019-04-09 16:12:33 cri


Da sanyin safiyar yau Talata aka gudanar da muhimmin taron kafa cibiyar nazarin dangantakar kasashen Sin da Afrika a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnatocin kasashen Sin da na Afrika, kwararru da masanan bangarorinn biyu, da kuma jami'an diplomasiyya na kasashen Afirka da AU da ke nan Beijing.

Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma darektan ofishin kwamitin harkokin waje na kwamitin tsakiya na JKS ya halarci bikin kafa cibiyar, tare da karanta wasikar shugaba Xi Jinping ta murnar kafuwar cibiyar.

Cikin sakon taya murnarsa, shugaba Xi Jinping ya ce,

"Kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya kana nahiyar Afrika shiyya ce dake kunshe da mafi yawan kasashe masu tasowa a duniya."

Makasudin kafa cibiyar nazarin Sin da Afrika wato "China-Africa Institutes" a Turance shi ne, domin nazarin muhimman bangarorin da suka shafi tsarin shugabanci da raya ci gaban kasashen Sin da Afrika.

Kafa cibiyar ya biyo bayan muhimman kudurori ne 8 wadanda shugaba Xi Jinping ya gabatar a lokacin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a Beijing 2018, wanda kuma batun kafa cibiyar na daya daga cikin kudurorin guda 8 da shugaba Xi ya ambata. Kafa wannan cibiya zai taimaka wajen kara karfin dangantaka tsakanin bangarorinn biyu da kuma kyautata huldar kut-da-kut tsakanin mutum da mutum na al'ummomin kasashen Sin da Afrika, in ji Yang Jiechi.

Farfesa Sarah Anyang Agbor kwamishiniyar hukumar kula da ci gaban kimiyya da fasaha ta kungiyar tarayyar Afrika AU wanda ta gabatar da jawabinta a madadin shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU a lokacin taron ta bayyana cewa, ta nuna matukar farin cikinta a madadin kungiyar tarayyar Afrika AU da shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat, bisa abin da ta kira karamcin da kasar Sin da al'ummar Sinawa ke nunawa kasashen Afrika, kana ta yabawa gwamnatin Sin bisa goron gayyartar da ta baiwa kungiyar ta AU a lokacin muhimmin taron kafa cibiyar nazarin Sin da Afrika. Ta ce, kungiyar AU tana matukar farin ciki bisa irin matuntawar da Sin ke baiwa kungiyar da kara janta a jiki don yin mu'amala tare da nufin inganta muradun al'ummomin Sin da na kasashen Afrika. Farfesa Sarah ta kuma yabawa kasar Sin bisa irin namijin kokarin da take wajen tallafawa al'ummomin Afrika a bangarori daban daban a shekaru masu yawa da suka shude.

Ta ce taron dandalin FOCAC na Beijing 2018, ya gabatar da wani muhimmin shiri na raya dangantakar bangarorin biyu da kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu na shekarar 2019 -2021, domin kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta fuskar musayar ra'ayoyi, da mu'amalar ciniki da tattalin arziki, ilmin kimiyya da fasaha, mutunta juna, samar da horo, da musayar kwarewa da ci gaba, kuma a cewarta wadannan su ne muhimman bangarori wadanda za su tabbatar da kara karfafa zumunci da samar da kyakkyawar makoma game da mu'amalar dake tsakanin kasashen Sin da Afrika a nan gaba, in ji Sarah Agbor.

A cewarta, AU a shirye take ta kara zurfafa mu'amalarta da kasar Sin wajen cimma nasarar ajandar nan ta AU ta samar da dawwamamman ci gaban raya kasashen Afrika nan da shekarar 2063, domin nahiyar Afrika ta yi amfani da kwarewarta da 'yan kasarta wajen gina ci gaban nahiyar wanda hakan shi ne zai tabbatar da nasarar bunkasuwar tattalinn arzikin nahiyar wanda yana daya daga cikin abin da al'ummar ke da muradinsa. Farfesa Sarah ta ce bunkasa ilmi zai taimaka wajen samun muhimman fasahohin da ake bukata wajen raya ci gaban nahiyar da samun arziki da amfani da dimbin albarkatun da nahiyar take da su.

Tsohon shugaban kasar Mozambique Joaqium Albertor Chissano, ya gabatar da jawabi a lokacin taron, inda ya tabo wasu daga cikin fa'idojin kafa cibiyar nazarin Sin da Afrika inda ya bayyana cewa, kafa cibiyar wani sabon mataki ne na kara dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika wanda zai taimakawa matasa da kwararrun masanan kasashen biyu wajen bunkasa moriyar al'ummomin kasashen biyu wato Sin da Afrika.

A cewarsa kafa cibiyar wani muhimmin tubali ne da zai kara kyautata mu'amalar tsakanin mutum da mutum na al'ummomin sassan biyu tare da samar da kyakkaywar makoma ga bil Adama musamman wajen raya ci gaban kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire da kuma samun moriya ga jama'ar kasashen Sin da Afrika.

Idan za'a iya tunawa a lokacin taron FOCAC na Beijing na 2018, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimman kudurori 8 karkashin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, cikin kuduroin 8 akwai batun kafa cibiyar nazarin Sin da Afrika wacce ake sa ran za ta mayar da hankali kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi bunkasa ci gaban kasashen biyu musamman batun mu'amalar ciniki da tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, yaki da talauci, kiyaye muhallin hallittu, da wanzar da zaman lafiya da tsaro da dai sauransu. Sama wakilan gwamnatoci, kwararru, jami'an diplomasiyya na kasashen Afrika sama da 40 ne suka halarci bikin kaddamar da cibiyar nazarin Sin da Afrika a birnin Beijing.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China