in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron dandalin Bo'ao na shekarar 2019
2019-04-11 14:51:11 cri

Bo'ao, kungiya ce mai zaman kanta dake shirya manyan tarukan shugabannin gwamnatoci, da 'yan kasuwa da masana dake yankin Asiya da sauran kasashe, don muayar ra'ayoyi da kan manyan batutuwa dake damun shiyyar da ma duniya baki daya.

Dandalin Bo'ao ko BFA a takaice, ya yi kama da dandalin tattalin arziki na duniya na Davos. Koda yake ana gudanar da taron dabdalin ne a garin Bo'ao dake lardin Hainan na kasar Sin, amma sakatariyar dandalin tana birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ne.

Dandalin yana kokarin hade tattalin arzikin shiyyar da ma manufofin kasashen Asiya waje guda. Bayanai na nuna cewa, tsohon shugaban kasar Philippines Fidel V.Ramos da tsoffin firaministocin kasashen Australia Bob Hawke da na Japan Morihiro Hosokawa ne suka gabatar da kafa dandalin. An kuma kaddamar da shi a watan Fabrairun shekarar 2001.

Jamhuriyar jama'ar kasar Sin kuma ta jagoranci kafa dandalin mai kunshe da kasashe da jihohin Australia 26 a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2001. An kuma gudanar da taron dandalin na farko a ranakun 12-13 ga watan Afrilun shekarar 2002.

Bisa al'ada, batutuwan da ake tattaunawa a taron dandalin, sun hada da tattalin arziki, batun hadewar shiyyar, yin hadin gwiwa, da al'umma da kuma muhalli.

A yayin taron dandalin na shekarar 2019 da aka gudanar tsakanin ranakun 26-29 ga watan Maris, ana saran gudanar da taruka 50 kan manyan batutuwa 5, ciki har da batun tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da hadin gwiwar shiyyar, da tafiyar da harkokinn kasa da kasa, da raya kirkire-kirkire da ci gaba mai inganci.

Taken taron na bana shi ne "makomar bai daya, da daukar matakai na bai daya, da samun ci gaba tare", wanda kuma ya samu halartar wakilai sama da 2000, da suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 60. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China