in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Kenya
2019-04-09 10:41:30 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana a birnin Nairobi a jiya Litinin cewa, a wadannan shekaru an kara raya dangantakar dake tsakanin Kenya da Sin, kana akwai kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar kasashen.

Shugaba Kenyatta ya bayyana yayin da yake karabar takardar nadin jakadan Wu Peng a matsayin jakadan Sin a kasar Kenya cewa, kasar Kenya tana godiya ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta kan yadda suke nuna goyon baya sosai ga kasar Kenya. Ya ce, yana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin don inganta hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin noma, ayyukan more rayuwa da sauransu, matakin da zai kara raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, jakada Wu Peng ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun sha ganawa, hakan ya inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kara yin imani da juna a fannin siyasa, da kara samun kyakkyawan sakamako kan hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Sin za ta ci gaba da yin amfani da damar raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wajen zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu don amfanawa jama'arsu yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China