Dickson Ruto, kwamandan dakarun AMISOM yace, aikin wanda ke gudana a garin Dhobley dake shiyyar Lower Jubba ana gudanar da shi ne a matsayin wani aikin hadin gwiwa tsakanin dakarun sojoji da fararen hula na AMISOM da hukumar gudanarwar yankin.
Ruto yace dakarun AU sun sha alwashin tabbatar da tsaron muhimman hanyoyin shigar da kayayyaki yankunan da kuma manyan cibiyoyin taruwar jama'a dake wajen garin Dhobley.
Mayakan 'yan ta'adda na Al-Shabab suna cigaba da takaita zirga zirgar jama'a tare da kwace ikon hanyoyin shiga yankunan, kamar yadda hukumomin yankunan da masu bada tallafin jin kai suka bayyana.