in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu yayin wani harin kunar bakin wake a Nijeriya
2019-04-08 13:47:50 cri
Mutane Akalla 3 sun mutu, sanadiyyar wasu tagwayen hare-hare da aka kai wata unguwa dake wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno, mai fama da rikici a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Majiyoyi daga jami'an tsaro sun bayyana cewa, wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin ranar Asabar da daddare a unguwar Muna Dalti.

Gidan talabijin na Channels dake kasar, ya ruwaito jami'an kai daukin gaggawa na jihar na cewa, harin ya yi sanadin mutuwar 'yan kungiyar civilian JTF 2, wato fararen hula masu taimakawa jami'an tsaro, tare da jikkata wasu mutane 45.

Rahoton gidan talabijin din ya kuma ruwaito Shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta jihar, Bello Dambatta, ya ce wasu 'yan kungiyar civilian JTF sun ga wasu mata biyu dauke da ababen fashewa, kuma sun yi kokarin dakatar da su, sai dai sun mutu tare da wani mutum guda, bayan tashin bam din.

Minti 5 ne tsakanin bam na farko da na biyu da 'yan kunanr bakin waken suka tayar a unguwar Muna Dalti.

Kawo yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai harin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China