in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sudan ta yi gargadi game da yuwuwar barkewar yakin basasa saboda siyasa
2019-04-08 13:41:22 cri

Minsiatan yada labarai na kasar Sudan Hassan Isma'il, ya yi gargadi game da yuwuwar barkewar yakin basasa saboda bambamcin ra'ayin siyasa.

Ministan ya zargi wasu bangarori na kasashen waje da kungiyoyin dake da alaka da kungiyar kwararru ta Sudan da bangaren adawa da karban kudade masu yawa domin gudanar da zanga-zanga a kasar.

Ya kuma zargi bangaren adawar da kin amincewa da tattauanawa da gwamnati.

Ya ce rashin amincewa da tattaunawa da gwamnati ba tare da bayar da kwararan dalilai ba ya nuna cewa bangaren adawar na bukatar hambarar da gwamnati ne kawai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China