in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Me ya jawo hankalin duniya wajen shigar da takardun lamuni na kudin Yuan na kasar Sin cikin ma'aunin jari na duniya na Bloomberg Barclays?
2019-04-08 14:45:55 cri

A farkon watan Afrilu da muke ciki ne, kasar Sin ta sake jawo hankalin duk duniya yayin da take kokarin kara bude kofarta ga ketare, wato aka fara sanya takardun lamuni na kudin Sin da gwamnatin Sin da ma bankuna masu tsara manufofin kasar suka bayar cikin ma'aunin jari na duniya na Bloomberg Barclays. Wakilin farko na asusun ba da lamuni na duniya na IMF da ke kasar Sin Alfred Schipke ya bayyana cewa, matakin ya zama tamkar ishara ga kasar Sin wajen shiga cikin tsarin hada-hadar kudi na duniya. Ban da wannan kuma, shahararriyar kafar watsa labaran kasuwanci ta duniya ta CNBC ta jaddada cikin rahotonta cewa, wannan wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka na bude kasuwar kudinta ga ketare.

Ma'aunin jari na duniya na Bloomberg Barclays daya ne daga cikin muhimman ma'aunan takardun lamuni guda uku na duk duniya. Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan jarin kasa da kasa da ke da nasaba da ma'aunin ya kai dala trilliyan biyar. Yadda aka shigar da takardun lamunin kasar Sin cikin ma'aunin ya shaida cewa, akwai yiyuwar masu zuba jari bisa ma'aunin, su sayi takardun lamuni na kudin Sin, hakan zai sa karin jari ya shiga kasuwar takadun lamuni ta kasar Sin. Don haka an yi hasashen cewa, shigar da takardun lamunin kasar Sin cikin ma'aunin Bloomberg Barclays ya shaida amincewar da kasuwar jarin duniya ta nunawa kasar Sin kan yadda ta bude kofarta ga ketare ta fuskar harkokin kudi. Hakika dai ma, kasar Sin ta cancanci yabo.

Da farko dai, Kudin Sin na shiga kasuwar duniya a kai a kai yadda ya kamata. Takardun lamuni na kasar Sin da aka shigar da su cikin ma'aunin Bloomberg Barclays a wannan karo takardun lamuni ne guda 364 na kudin Sin, kuma sakamako ne da aka samu bisa yunkurin amfani da kudin Sin a kasuwar duniya da kasar Sin ke shimfidawa. A watan Oktoban shekarar 2016, a hukumance kudin kasar Sin RMB ya fara aiki a matsayin kudaden ajiya na ketare(SDR)na asusun IMF, wanda yawansa ya kai kashi 10.92 cikin dari. Tun daga wancan lokaci ne, kasashe daban daban suka fara amincewa da matsayin kudin Sin na kudaden ajiya na ketare. yawan kudin Sin da manyan bankunan kasashen waje suka ajiye ya karu da kashi 100 cikin dari. A waje daya kuma, sakamakon babban tasirin tattalin arzikin kasar Sin ke yi kan tattalin arzikin duniya, masu zuba jari na ketare na kara bukatar kadarorin kasar Sin.

Na biyu kuma shi ne, kasuwar takardun lamunin kasar Sin na da karfin takara a duniya bisa girmanta da ma yawan ribar da ake samu. Ya zuwa karshen watan Fabrairun bana, darajar yawan takardun lamuni da ya rage a kasuwar kasar Sin ya kai kimanin dala triliyan 13, lamarin da ya sa kasar Sin ta zama kasuwa mafi girma ta uku a duk duniya ban da Amurka da Japan. Bayan watanni 20 da shigar da takardun lamunin kasar Sin cikin ma'aunin Bloomberg Barclays, yawan takardun zai kai kashi 6 cikin dari, inda ake saran takardun lamuni na kudin Sin zai zama takardun lamuni mafi muhimmanci na hudu a duniya ban da na Dala, EURO, da ma kudin Japan. Bisa wani sakamakon binciken da Bloomberg ya bayar a watan Fabrairun bana, masu zuba jari na kasashen Asiya da yawansu ya zarce kashi 67 cikin dari sun nuna aniyarsu ta sayen takardun lamunin kasar Sin a shekarar da muke ciki.

Na uku shi ne, abun da ya shafi yawan ribar da ake samu. Yawan ribar da ake samu ta hanyar sayen takardun lamunin kasar Sin na tsawon shekaru 10 ya zarce na Amurka, Jamus da ma Japan. Li Bing, babban daraktan reshen kamfanin Bloomberg da ke kasar Sin ya fayyace a kwanakin baya cewa, yawan ribar da aka samu ta hanyar sayen kadarorin Sin bisa ma'aunin Bloomberg Barclays ya kai kashi 3.45 cikin dari a shekarar 2018, yayin da jimillar ribar da aka samu kan kadarorin Amurka ta kai kashi 0.01 cikin dari kawai. Babu shakka kididdigar za ta ba da jagoranci sosai wajen zuba jari.

Shigo da jarin ketare mataki na farko ne da gwamnatin kasar Sin ke dauka wajen bude kasuwar kudinta ga waje, baya ga yadda take kokarin hada kasuwar takardun lamuninta da kasuwannin ketare, da ma daidaita tsarukanta don dacewa da ayyukan masu zuba jari na ketare. Ana sa ran gwamnatin Sin za ta fitar da cikakken manufofi da matakai a fannonin kara bullo da bayanan kamfanoninta, da ma kara yawan hanyoyin kawar da tasirin da kwararar kudi ke iya haifarwa kasuwar kudi, a kokarin kyautata kasuwarta. A watan Fabrairun bana, Shugaba Xi Jinping na Sin ya taba nanatawa a gaban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin cewar, ya kamata Sin ta yi nazari kan fitar da sabbin matakan bude kofarta bisa sauyawar harkokin kudi na duniya da ma bukatun cigaban kasar. Kasuwar da ke da kudin da ke iya kaiwa da kawowa, za ta zama mai karfi sosai. Shugaba Xi ya taba bayyanawa cikin jawabinsa na sabuwar shekara cewar, kasar Sin da ke da kudin kaiwa da kawowa, tabbas na cike da karfin samun ci gaba da wadata. Yadda za a bude kasuwar takardun lamunin Sin ga waje, ko shakka babu zai sa kaimi ga karin ire-iren kadarorin duniya, da ma tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya lami lafiya kuma yadda ya kamata.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China