in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin zata bunkasa kanana da matsakaitan kamfanoni
2019-04-08 10:21:05 cri

Kasar Sin ta bayyana wasu ka'idoji da zasu taimaka wajen bunkasa cigaban kanana da matsakaitan kamfanonin kasar wato (SMEs).

A matsayinsu na muhimman ginshikan raya cigaban tattalin arziki da yanayin zamantakewar al'umma, kanana da matsakaitan kamfanoni suna ba da gagarumar gudunmowa wajen samar da guraben ayyukan yi, inganta rayuwar jama'a, da kuma bunkasa harkokin sana'o'in dogaro da kai da kirkire-kirkire, inji wata sanarwar hadin gwiwa wanda babban ofishin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na majalisar gudanarwar kasar Sin suka fitar.

Haka zalika, ka'idojin da aka fitar sun bukaci a kara mayar da hankali wajen tunkarar matsalolin dake kawo cikas ga cigaban kanana da matsakaitan kamfanoni, kamar tsadar kayayyakin gudanarwa, da wahalhalun da ake cin karo dasu wajen neman kudaden gudanarwa da kuma karancin kirkire-kirkire.

Bugu da kari, za'a cigaba da daukar kwararan matakai domin kyautata hanyoyin da SMEs ke samu kudaden gudanarwarsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China