in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun ci gaban tattalin arzikin Sin mai inganci ta hanyar habaka bude kofa a bangaren aikin hidima
2019-04-05 16:42:10 cri

A cikin shekaru 40 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba ba tare da rufa rufa ba, a don haka nan gaba dole ne za a kara habaka ci gaban tattalin arzikin kasar bisa tushen bude kofa ga kasashen waje.

A cikin rahoton babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an gabatar da cewa, kasar Sin za ta kara bude kasuwarta, haka kuma za ta kara bude kofa a bangaren samar da hidima. Shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ma ya taba bayyanawa a yayin taron dandalin Asiya na Boao da kuma bikin bude CIIE cewa, kasarsa za ta kara bude kofa ga kasashen waje kan aikin samar da hidima, ta yadda za a tsara sabon tsarin bude kofa ga kasashen waje a kasar ta Sin daga duk fannoni.

Aikin samar da hidima zai taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasar a nan gaba, haka kuma, wani muhimmin bangare ne da ke cikin ayyukan da ake gudanarwa yayin da ake kokarin cimma burin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci. A shekarar 2015, yayin da ake tsara tsarin bude kofa a bangaren samar da hidima wanda zai dace da bukatun ka'idojin kasa da kasa, tare kuma da ba da gudumowa kan aikin tsara sabon tsarin tattalin arzikin kasar Sin ba tare da rufa rufa ba, birnin Beijing ya fara aiwatar da manufar zurfafa gyare-gyare da bude kofa a bangaren samar da hidima, mataimakin shugabar hukumar kasuwancin birnin Liu Meiying ta bayyana cewa, "Kara bude kofa ga kasashen waje a bangaren samar da hidima, muhimmin mataki ne da muka dauka domin ingiza ci gaban tattalin azikin Beijing mai inganci, dalilin da ya sa haka shi ne domin za mu kara habaka kasuwarmu ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, hakan zai sa mu samu karin jari da za a zuba, tare kuma da cimma burin samun ci gaban tattalin arzikin birnin mai inganci yadda ya kamata, kana za mu kara kyautata manufar zuba jari da kasuwanci ta hanyar yin kirkire-kirkire, ta yadda za mu biya bukatun ka'idojin kasa da kasa, tare kuma da samar da tabbaci ga ci gaban tattalin arziki mai inganci a bangaren manufa, ban da haka, za mu kara kyautata yanayin kasuwanci domin taimaka da kuma kara kuzari ga ci gaban tattalin arziki mai inganci a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin."

A yankin Shunyi na birnin, akwai wani kamfanin gyara na'urorin jiragen sama, wanda kamfanin BGAC na birnin Beijing da kamfanin gyara na'urorin jiragen sama na AIR Faransa-KLM, suka kafa cikin hadin gwiwa, babban manajan kamfanin Wu Yutong ya bayyana cewa, kafin shekarar 2015, gwamnatin kasar Sin ta hana kamfanin jarin waje ya mallaki hannun jarin da yawansa ya kai sama da kaso 51 bisa dari a sana'ar gyara na'urorin jiragen sama, a don haka zai yi wahala kamfanin kasar Sin ya yi hadin gwiwa da kamfanin kasar waje a bangaren, Wu Yutong yana mai cewa, "Bisa ka'idar hukumar jirga-jirgar jiragen saman fasinjan kasar Sin mai lamba 110, ba zai yiyu ba kamfanin kasar waje ya zuba jari ya zarta kaso 49 bisa dari a kasar Sin ba, shi ya sa kamfanin waje ya nuna rashin jin dadi kan wannan batun, har muka sha tattauna,amma ba mu cimma matsaya guda ba."

Abu mai faranta rai shi ne tun daga shekarar 2015, birnin Beijing ya fara aiwatar da sabuwar manufar da abin ya shafa, sai dai kamfanin BGAC na birnin Beijing da kamfanin gyara na'urorin jiragen sama na AIR Faransa-KLM sun fara gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu cikin sauri.

Rukunin ABB, shahararren babban kamfanin fasaha mai samar da na'urar mutum mutum da ake amfani da su masana'antu wanda ke gudanar da harkokinsa a kasashe da shiyyoyi sama da 100 a fadin duniya, a cikin shekarun baya bayan nan, mataimakin shugaban kamfanin reshensa na kasar Sin Lars Eckerlein ya bayyana cewa, "Kamfaninmu yana gudanar da harkokinsa a kasar Sin lami lafiya, saboda birnin Beijing ya ba mu munufar gatanci a bangaren samar da hidima, ko shakka babu muna cike da imani matuka kan ci gaban kamfaninmu a kasar Sin, a don haka kamfanin ABB zai kara zuba jari a nan, domin taka rawa ga ci gaban Beijing mai inganci."

Ya zuwa shekarar 2018, adadin jarin wajen da birnin Beijing ya samu ya kai kaso 90 bisa, adadin GDP da birnin ya samu a bangaren samar da hidima ya kai kaso 80 bisa dari, cinikayya a bangaren kuma ta kai kashi 1 bisa 5 na daukacin adadin fadin kasar Sin, ana iya cewa, habaka bude kofa a bangaren samar da hidima yana da babbar ma'ana ga ci gaban tattalin arzikin kasar mai inganci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China