in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya dace a kara habaka moriyar bangarorin Sin da Amurka
2019-03-30 13:44:23 cri

 

An kammala tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama'an kasashen Sin da Amurka karo na 8 a nan birnin Beijing a jiya Juma'a. An shafe kwanaki biyu ana tattaunawar wadda ke karkashin jagorancin mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firayin ministan kasar kuma jagoran bangaren kasar Sin kan tattaunawar tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka wato Liu He, da wakilin cinikayyar Amurka Robert Lighthizer da ministan kudin kasar Steven Mnuchin, inda sassan biyu suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar da za su daddale, haka kuma sun samu sabon ci gaba a kai.

 

 

A cikin watanni hudun da suka gabata, an yi tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama'an kasashen Sin da Amurka har sau hudu, yanzu haka an shiga mataki mafi muhimmanci ke nan. A cikin tattaunawar karo na 7 da sassan biyu suka yi, sun yi shawarwari kan batutuwan da suka shafi sayayyar fasahohi, da kare ikon mallakar fasaha, da matakan da za a dauka domin kayyade shigo da kayayyaki daga ketare da ba na karbar harajin kwastam ba, aikin samar da hidima, da aikin gona da farashin kudin musaya da sauransu, sun kuma samu babban ci gaba. Yayin tattaunawar karo na 8 kuwa, sassan biyu sun ci gaba da tattaunawa kan batutuwan, har ma sun samu sabon ci gaba, hakan ya nuna cewa, za su cimma muradun da shugabannin kasashen biyu suka tsara a kasar Argentina.

Hakika abu ne mai wahala samun ci gaban tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama'an kasashen biyu, duk da cewa, sun yi shawarwarin ne a asirce, an lura cewa, sassan biyu sun sanya kokari matuka kuma sun hanzarta tattaunawar, domin rage lokacin da suke bukata, misali yayin tattaunawa karo 8 da aka kammala jiya, sun sauya liyafar maraba ga baki zuwa abincin dare, inda sassan biyu suka tattauna yayin cin abincin, kana ba su shirya bikin kaddamar da tattaunawa ba, sai kawai suka fara aiki kai tsaye ba tare da bata lokaci ba.

Duk wadannan sun nuna cewa, sassan biyu wato Sin da Amurka sun sanya kokari matuka, saboda ya kasance babban bambancin dake tsakaninsu, misali tsarin zaman takewar al'umma da al'adu da yanayin kasa da ci gaban kasa da sauransu, kuma batun tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka ba huldar sayayya ne kawai ba, yana da sakarkakiya sosai, a don haka ya zama wajibi su yi ayyuka da yawan gaske cikin gajeren lokaci. Ana iya cewa, a cikin kwanaki 120 da suka gabata, tawagoyin wakilan kasashen biyu sun yi aiki ba rana ba dare.

Abun farin ciki shi ne sun samu ci gaba a bayyane.

 

Bisa alkaluman da ma'aikatar kasuwancin Amurka ta fitar a ranar 27 ga wata, an ce, adadin kayayyakin da kasar ta fitar zuwa kasashen waje a watan Janairun da ya gabata ya karu da kaso 0.9 bisa dari, wato ya kai dala biliyan 207 da miliyan 300, amma adadin kayayyakin da kasar ta fitar zuwa ga kasar Sin ya ragu zuwa dala biliyan 7 da miliyan 100, adadin da ya kai matsayi mafi kankanta tun bayan shekarar 2010. Kana bisa alkaluman da kasar Sin ta samar, an ce, a cikin farkon watanni biyu na bana, adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka ya ragu da kaso 19.9 bisa dari. Ban da haka kuma, bisa dalilin tsananin huldar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka a halin da ake ciki yanzu, an yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a bana za ta ragu daga kaso 3.5 bisa dari zuwa kaso 3.3 bisa dari.

An lura cewa, kara karbar harajin kwastam tsakanin Sin da Amurka ya kawo babbar illa ga tattalin arzikin kasashen biyu, shi ya sa wajibi ne a cimma muradun shugabannin kasashen biyu tun da wur wuri. Yanzu sassan biyu sun riga sun shiga mataki mafi muhimmanci, a don haka ya dace su kara habaka moriyarsu duka. Misali, Amurka ta fi mai da hankali kan batutuwan da suka shafi yadda za a kare ikon mallakar fasaha da shiga kasuwar kasar Sin da tsarin kasuwancin da za a yi amfani da shi, to, muddin dai wadannan batutuwan suka dace da manufar kasar Sin ta zurfafa gyare-gyare da kara bude kofa, babu shakka za a daidaita su sannu a hankali.

A mako mai zuwa, za a ci gaba da gudanar da tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama'an kasashen biyu karo na 9 a Washington. A don haka ya kamata sassan biyu su kara kokari domin samun moriya tare, ta hanyar cimma muradun shugabannin kasashen biyu.

Bisa nata bangare, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da nuna sahihanci domin daddale yarjejeniya mai amfanawa juna, idan ba su iya cimma burin ba, kasar Sin ita ma ba za ta damu ba ko kadan, saboda Sinawa sun fahimci cewa, samun ci gaba a kasarsu, shi ne abu mafi muhimmanci a gare su.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China