in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne a tuna tare da martaba shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa
2019-03-25 14:25:23 cri

Taron manema labaran da aka yi a yayin taron kolin G20 da ya gudana a Buenos Aires na kasar Argentina a shekarar 2018, ya jawo hankulan sosai. Mr. Wang Yi, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, da takwaransa na Faransa Jean-Yves Le Drian da Mr. Antonio Guterres, babban sakataren MDD sun shaidawa taron manema labarai na kasa da kasa , cewar za su yi hada kai tare wajen cika alkawarin da aka yi don tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya cikin hadin gwiwa. Baya ga sanar wa duniya cewa bangarorin uku na ba da muhimmanci sosai ga gwagwarmayar tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya, ya kuma alamta cewa, kasashen Sin da Faransa suna hada kai sosai wajen tinkarar matsalar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, "Kasashen Sin da Faransa abokai ne na musamman". Sinawa su kan yaba da kyawawan abubuwan da wani ya yi musu. A lokacin da suke ambaton kasar Faransa, su kan jaddada cewa, kasar Faransa ita ce kasar farko daga cikin kasashen yammacin duniya da ta kulla dangantakar jakadanci da Jamhuriyar Jama'ar Sin. Sannan ita ce kasar farko da ta bude hanyar jirgin sama tsakaninta da sabuwar kasar Sin daga cikin kasashen yammacin duniya, kana ita ce ta farko da ta amince da kebe shekara daya domin nune-nunen al'adun kasar Sin da kuma kafa cibiyar al'adun Sinawa a yankinta, kana ita ce ta farko da ta kafa sashen koyon harshen Sinanci a jami'arta daga cikin kasashen yammacin duniya.

A shekarun 60 na karnin da ya gabata, bisa kwazo da karfin hali, janar Charles de Gaulle ya amince da kulla dangantakar diflomasiyya daga dukkan fannoni tsakanin kasar Faransa da Jamhuriyar Jama'ar Sin. Lamarin ya rage gibin dake tsakanin kasar Sin da kasashen yammacin duniya sakamakon yakin cacar baki, ya kuma kusanto da kasar Sin da kasashen yammacin duniya. Sabo da haka, al'ummar Sinawa su kan nuna godiya ga kasar Faransa.

Ko shakka babu, dalilin da ya sa dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa ta samu ci gaba da karfafuwa shi ne, kasashen biyu su kan bude kofofinsu ga juna da kuma yin hadin gwiwa tsakaninsu. A shekarar 1978, wato lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga ketare, marigayi Deng Xiaoping, muhimmin shugaban kolin kasar Sin ya shelanta cewa, kasar Sin za ta shigo da fasaha daga kasar Faransa domin gina wata tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya a kasar Sin. Sanin kowa ne cewa, gina tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya ba abu ne da aka saba gani a kullum ba, kana ba hadin gwiwar kasuwanci da aka saba gani a yau da kullum ba. Masu 'yan fashin baki sun nuna cewa, dalilin da ya sa kasashen Sin da Faransa suka yi hadin gwiwa wajen gina tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya shi ne gwamnatocin kasashen biyu suna amincewa da juna a fannin harkokin siyasa. A bara, darajar cinikayyar da aka yi tsakanin kasashen biyu ta kai dalar Amurka biliyan 62.9, wato ya kai wani sabon matsayin da ba a taba gani a tarihi ba. Sannan yawan birane da larduna na kasashen biyu da suka kulla zumunta ya kai 102, yawan daliban kasar Sin wadanda suke karatu a kasar Faransa ya kai kusan dubu 40, a yayin da daliban Faransa fiye da dubu dari 1 suke karatu a nan kasar Sin. Wadannan ayyukan hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da kuma al'ummomin kasashen biyu sun kara kusanto da kasashen biyu.

Wani abin jaddadawa shi ne, ko da yake al'amura na sauyawa a kasashen duniya, muddin kasashen Sin da Faransa suka tuna da kuma aiwatar da muhimman ka'idoji masu muhimmanci, tabbas "huldar musamman" dake tsakanin kasashen biyu za ta karfafu har ma ta ci gaba. Wadannan muhimman ka'idoji su ne "muhimman abubuwa 4" da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya zayyana, wato tabbatar da 'yancin kasa, bude kofa domin neman nasara tare, da hakuri da kuma koyi da juna, sannan sauke nauyin dake bisa wuyansu tare. Muddin kasa ta tabbatar da 'yancin kanta, to, za ta iya sauke nauyin dake bisa wuyanta, kuma za ta iya tsayawa kan matsayin da ya kamata ta dauka, ta yadda za a iya magance matsalar da ka iya kunno kai a halin da ake ciki. Muddin aka yi hakuri da juna, za a iya bude kofofin juna, ta yadda za a iya samun nasara tare.

A cikin shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya gabata, akwai wata kyakkyawar ka'ida, wato "tattaunawa tare, raya harka tare, sannan da raba moriya". Wannan ya alamta zaman daidai wa daida, da hada kai da kuma cin gajiya tare. Kasashen Sin da Faransa suna amincewa da juna a fannin siyasa. Bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", kasar Faransa za ta iya taka muhimmiyar rawar da ake fata, kuma za ta iya daukar karin matakan yin hadin gwiwa da Sin a fannin kasuwar wani bangare na daban a lokacin da take bunkasa "ziri daya da hanya daya" da bangaren Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China