"Na yi tattaunawar abokantaka mai zurfi da kuma ganawa da jami'an kasar Italiya, ciki har da shugaban kasar," Xi ya bayyana hakan ne a cigaba da ziyarar aikin da yake yi ta kwanaki hudu a kasar Italiya. Kafin ya bar kasar, ya halarci wata gagarumar liyafar girmamawa wanda takwaransa na kasar Italiya Sergio Mattarella, ya shirya masa.
Yana mai cewa, "amincewar juna da kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a dukkan fannoni tana kara zurfafa," Xi, ya kuma bukaci kasashen Sin da Italiya dasu kara zurfafa mu'amalarsu domin kara kyautata matsayin alakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.