in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD yayi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a kauyen kasar Mali
2019-03-24 16:08:13 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres a ranar Asabar yayi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi wa a'lumma a wani kauyen kasar Mali, inda rahotanni ke nuna cewa an hallaka fararen hula kimanin 134 a kauyen.

Babban sakataren MDD yayi matukar nuna damuwa a yayin da ya samu rahoton kisan fararen hula 134, wanda ya hada da mata da kananan yara, yayin da aka jikkata wasu mutanen akalla 55 bayan wani hari da aka kaddamar da safiyar wannan ranar a kauyen Ogossagou Peulh, dake yankin Mopti a tsakiyar Mali," Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren ne ya bayyana cikin wata sanarwa.

Babban sakataren ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa dasu, da kuma al'ummar Mali da gwamnatin kasar, kana yayi fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka samu raunuka.

Jami'in MDD ya bukaci hukumomin kasar ta Mali dasu kara kokari wajen tattabatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kasar ta Mali, inji Haq.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka yiwa kauyen kawanya inda suka kai harin kan gidajen mazauna kauyen na Ogossagou dake shiyyar Mopti. An shirya kai harin ne kan al'ummar Fulani.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China