Bangarorin biyu sun amince su hada hannu wajen lalubo mafitar da ta dace da matsalolin Idlib, babbar tungar 'yan tawaye da ta rage a Syria, da yankin gabashin kogin Euprate, wadanda ke karkashin ikon dakarun Syria da Amurka ke goyawa baya.
Sun bayyana cewa, Amurka ce ke mara baya ga kungiyar SDF a ayyukan da take a gabashin kogin Eupharate dake gabashin Syria, yayin da Turkiyya kuma ke da tasiri kan 'yan tawayen dake Idlib.
Shugaba Assad da Ministan tsaro na Rasha, sun kuma tattauna kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2 a yaki da ta'addanci da nasarorin da aka samu kan yaki da kungiyar IS da kungiyar Nusra Front ta Syria, dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda. (Fa'iza Mustapha)