in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin nune-nune mai taken "Sojojin Sin da ke kiyaye zaman lafiyar duniya"
2019-03-19 14:37:27 cri



A jiya Litinin, a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka da ke Adis Ababa, babban birnin kasar Habasha, an kaddamar da bikin nune-nune da aka sanya masa jigon "Sojojin kasar Sin" da ke kiyaye zaman lafiyar duniya, bikin da sashen kula da harkokin siyasa na kwamitin soja na koli na gwamnatin kasar Sin ya shirya tare da hadin gwiwar tawagar kasar Sin da ke kungiyar ta tarayyar Afirka.

Za a shafe tsawon kwanaki biyar ana gudanar da bikin, kuma bikin ya nuna hotuna sama da 60 tare kuma da hotunan bidiyo, don nuna yadda sojojin kasar Sin ke kokarinsu na kiyaye zaman lafiyar duniya. Mutane sama da 200 sun halarci bikin kaddamar da nune-nunen, ciki har da makaddashin shugaban tawagar kasar Sin da ke tarayyar Afirka, Chen Xufeng, da mukaddashin shugaban kwamitin kula da zaman lafiya da tsaro na hukumar tarayyar Afirka Admore Kambudzi, da shugaban tawagar wakilai masu kula da harkokin labarai na rundunar sojan kasar Sin babban kanar Mao Naiguo da ma jami'an tarayyar Afirka da wakilan mambobinta.

A bikin kaddamar da nune-nunen, mukaddashin shugaban tawagar kasar Sin da ke tarayyar Afirka, Chen Xufeng ya bayyana cewa, kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiyar duniya, musamman ma ga kasashen Afirka. Tun daga shekarar 1990, bi da bi sojojin kasar Sin sun halarci ayyukan kiyaye zaman lafiya 24 na MDD, kuma akasarinsu a kasashen Afirka ne suka aiwatar. Kullum kasar Sin na fatan ba da gudummawarta ga kiyaye zaman lafiya da ci gaba a Afirka.

"Daga cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya 24 na MDD da kasar Sin ta halarta, akwai 16 da aka aiwatar da su a kasashen Afirka. Har wa yau, sojojin kiyaye zaman lafiya da yawansu ya kai dubu 39 ne kasar Sin ta tura, wadanda daga cikinsu aka tura dubu 32 zuwa kasashen Afirka. Za mu mara wa tarayyar Afirka da kuma kasashen Afirka baya a kokarinsu na kiyaye zaman lafiya da kuma neman ci gaba, za mu kuma bai wa kasashen Afirka fifiko tare kuma da samar musu taimako amma ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba. Hakan kuma ya kasance babban dalilin ci gaban hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka cikin dorewa."

A nasa bangaren, makaddashin shugaban kwamitin kula da zaman lafiya da tsaro na hukumar tarayyar Afirka, Mr. Admore Kambudzi a nasa jawabin ya bayyana godiya ga kasar Sin game da yadda ta dade take samar da taimakonta ta fannin kiyaye zaman lafiya da tsaro a kasashen Afirka, ya ce, "Bikin da aka kaddamar a wannan karo ya sake shaida cewa, tuntubar juna a tsakanin sassa daban daban, zai iya karfafa huldar da ke tsakaninsu. Sin babbar kawarmu ce, wadda a cikin shekaru 20 da suka wuce, take ta samar da tallafi ga kasashen Afirka ta fannonin da suka hada da zaman lafiya da tsaro. A madadin tarayyar Afirka ina wa gwamnatin kasar Sin godiya kan taimakon da ta samar wa tarayyar Afirka, taimakon kuma da ta samar bisa tushen rashin tsoma baki cikin harkokin kasashen, tare kuma da yin la'akari da hakikanan bukatun tarayyar Afirka. Kasar Sin na iya zama misali wajen hulda da kasashen Afirka."

A wajen bikin, hotunan da aka nuna dangane da yadda likitocin rundunar sojan kasar Sin suka samar da gudummawarsu wajen yaki da cutar Ebola a Liberia da yadda sojojin ruwa na kasar Sin suka ba da kariya ga jiragen ruwan kasuwanci da ke mashigin tekun Aden da sauransu, sun burge masu kallo matuka. Kanar Mamane Souley, shugaban tawagar jami'an tsaro a Adis Ababa, wanda kuma shi ne wakilin jamhuriyar Nijer a tarayyar Afirka ta fannin soja, yana ganin cewa, bikin ya samar da wata kafa ta fahimtar kokarin da kasar Sin ke yi ta fannin zaman lafiya da tsaro, ya ce, "Sin babbar kawar kasashen Afirka ce, kuma na yi farin ciki da samun wannan damar fahimtar taimakon da sojojin kasar Sin suka samar wa kasashen Afirka ta fannin zaman lafiya da tsaro. A matsayina na jami'in tsaro, na taba gane ma idona yadda bangarorin biyu ke zumunta da juna a birnin Douala. Kasancewarta babbar kawar kasashen Afirka, kasar Sin ta taka rawar gani."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China