in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitancin gargajiya na kasar Sin ya shahara a Nijeriya
2019-03-18 14:11:47 cri

An bude asibitin farko mai rejista a hukumance, dake bada magungunan da kuma amfani da dabarun kiwon lafiya irin na kasar Sin hade da na kasashen yammacin duniya ne a can cikin unguwar Jabi dake Abuja, babban birnin Nijeriya.

wasu Sinawa ma'aurata ne suka kafa asibitin da ake wa lakabi da 'The Eastern and Western Hospital', wato asibitin da ya kunshi dabarun kiwon lafiya na Gabashi da Yammacin duniya, a shekarar 2017, domin samar da mafita ga matsalolin lafiya ta hanyar rungumar magungunan da dabarun kiwon lafiya na bature da na gargajiya na kasar Sin.

Asibitin The Eastern and Western Hospital, na amfani ne magungunan da dabarun kiwon lafiya na gargajiya na kasar Sin kamar su yin allura na acupuncture da tausa da sauransu.

Wata ma'aikaciyar gwamnati a kasar, mai suna Aisha Dogo, ta shafe kimanin shekaru 9 tana fama da matsanancin ciwon baya, wanda ya tilasta mata neman magani a asibitoci da dama dake ciki da waje kasar, sai dai hakarta ba ta cimma ruwa ba.

A kan magance ciwon baya wanda matsalar laka ke haifarwa ne ta hanyoyi biyu, wadanda suka hada da shan maganin kashe radadin ciwo da kuma tiyata.

Marasa lafiya da dama a fadin kasar ciki har da Aisha Dogo na fama da wannan ciwo, sai dai kuma yana iya dawowa bayan yin tiyata.

A daidai lokacin da Aisha Dogo ke gab da cire tsammani daga samun sauki ne ta yi nasarar karanta labarin asibitin ta kafar intanet tare da gano yadda ya zama wurin zuwan marsa lafiya a kasar mai dimbin jama'a dake yammacin Afrika.

Aisha Dogo ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ta fara zuwa asibitin ne saboda ta je asibitoci tare da shan magunguna da dama ba tare da samun dauwamamiyar mafita ba. Da take bayani game da lokacin da ta fara zuwa asibitin kasa da watanni 2 da suka gabata, ta kara da cewa, ta je asibitin ne da tarin matsaloli, kuma kawo yanzu, tana jin dadin yadda ta ke samun sauki.

Wani likitan bature da ya yi karatu a Amurka Muhammed Ibrahim, ya ce bambancin dake tsakanin dabarun kiwon lafiya na yammaci da gabashin duniya shi ne, dabarun bature ya fi mai da hankali kan warkarwa ko kuma shawo kan cuta, yayin da likitancin gargajiya na kasar Sin ke mayar da hankali kan kariya da kula da lafiya.

Cikin shekaru da dama, al'ummar Nijeriya masu yawa, sun gano likitancin gargajiya na kasar Sin, sai dai butakarsa na kara karuwa a baya bayan nan, inda marasa lafiya da dama suka gano cewa yana mayar da hankali ne kan kula da lafiyar jiki.

Andy Yuan, Likitan gargajiya na kasar Sin da ya assasa asibitin tare da mai dakinsa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a lokacin da ya bude asibitin shekaru 2 da suka gabata, a kullum, mara lafiya daya suke samu. Amma yanzu, adadin marasa lafiya da suka yi rejista da su ya kai 2,500, inda daruruwa daga cikinsu ke zuwa daga biranen dake fadin kasar.

Andy Yuan wanda shi ne likita na farko na kasar Sin da aka tantance a kasar, ya ce sun yanke shawarar zuwa Nijeriya ne saboda mutane a can na bukatar ayyukansu. Ya ce a can akwai asibitocin da likitocin bature, amma kuma bukatar wani nau'in lafiya na daban, kamar na gargajiya na kasar Sin na da yawa, domin mutane na bukatar kula da lafiyar jikinsu.

Ya kara da cewa, saboda sun mallaki ilimin likitancin bature da na gargajiya na kasar Sin ne ya sa shi da matarsa, hade dabarun biyu a asibitin domin samun ingantaccen sakamako, la'akari da cewa, dukkan dabarun biyu na da iyakoki.

Likitan ya ce, 'yan Nijeriya da dama suna son magungunan gargajiya na kasar Sin, kuma sun dade suna nema. Inda ya ce su kan yi ta nema a shafukan intanet, kuma su kan ji dadi idan suka je asibitin suka tarar da likitoci Sinawa ne.

Duk da cewa wasu 'yan Nijeriya na tantamar ingancin magaungunan, da ma tsarin likitancin gargajiya na kasar Sin, mutane da dama na son gwadawa.

Umar Iro, wanda shi ma ke ganin likita a asibitin, ya ce da farko ya ji tsoron acupunture, saboda ya ga hotuna da bidiyon yadda ake sokawa mutane allura a duk jikinsu, amma yanzu bayan ya gwada, ya ji dadinsa kwarai.

Daga cikin dabarun kiwon lafiya na likitancin gargajiya na kasar Sin, acupuncture ba marasa lafiya kadai yake jan hankali ba, domin dabarar na burge gogaggun likitoci.

Okosun O'casey, likita a asibitin na The Eastern and Western Hospital, ya ce duk da an dauke shi aiki ne a matsayin likitan bature, abu ne mai wuya ya kasa hadawa da dabarun likitancin gargajiya, saboda akwai wasu bangarorin kula da marasa lafiya da likitancin bature bai tabo ba har yanzu.

A cewar Rantiola Ogun, kwararen likita da ya yi karatu a Amurka, likitancin gargajiya na kasar Sin na tafiya ne kafada da kafada da tsarin kiwon lafiyar kasusuwa ko kwarangwal, saboda abun da ya fi mayar da hankalinka shi ne kasancewa cikin koshin lafiya, ya na mai bayyana asibitin 'The Eastern and Western Hospital' a matsayin na daban daga cikin jerin asibitocin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China